Miji Ya Fadi Yadda Ya Kama Matarsa Dumu-Dumu Tana Saduwa da Dan Uwansa, Ya Nemi Saki a Kotu

Miji Ya Fadi Yadda Ya Kama Matarsa Dumu-Dumu Tana Saduwa da Dan Uwansa, Ya Nemi Saki a Kotu

  • Wani Magidanci ɗan kasuwa, Justine Onu, ya nemi wata Kotu a Abuja ta raba aurensa da Joyce bisa zargin ganinta ta kwanta da ɗan uwansa
  • Mutumin ya faɗa wa Alkali cewa matar bata kula da shi, yayansa da sauran iyalai, burinta kawai ta kwanta kowa ta samu
  • Sai dai a bangaren wacce ake tuhuma, ta musanta zargin da mijin ke mata, Alkali ya dage zaman zuwa 8 ga Nuwamba, 2022

Abuja - Wani Magidanci ɗan kasuwa, Justine Onu, ranar Litinin ya roki Kotun Kostumare dake zama a Jikwoyi, babban birnin tarayya Abuja, ta raba aurensa da Matarsa mai suna Joyce a takaice.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Magidancin ya roki Kotu ta datse igiyoyin aurensu ne bisa zargin ya kamata dumu-dumu tana saduwa da ɗan uwansa.

Kara karanta wannan

2023: Dan Allah Ku Yafe Mun Kura-Kuran Da Na Yi A Mulkina, Gwamnan Arewa Ya Roki Mutanen Jiharsa

Gudumar Kotu.
Miji Ya Fadi Yadda Ya Kama Matarsa Dumu-Dumu Tana Saduwa da Dan Uwansa, Ya Nemi Saki a Kotu Hoto: premiumtimesng
Asali: Twitter

Magidancin ya shaida wa Kotun cewa matarsa wata macece mai son yin jima'i da kowane mutun ta haɗu da kuma maganar gaskiya ya gaji da haƙuri da aurensu.

Mista Onu ya ƙara da gaya wa Kotu cewa ta kai ga ya kamu da ciwan hawan jini sakamakon halin mai ɗakinsa nA kwanciya da mutane barkatai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da ƙari Magidancin ya ce matarsa wata macece da bata damu da alhakin dake kanta ba kuma bata kula da 'ya'yan da Allah ya basu ko ta girka wa iyalansa abinci.

Shin matar da ake zargin ta amsa laifinta?

Amma a nata ɓangaren, matar da ake ƙara Joyce ta musanta baki ɗaya tuhume tuhumen da Mijinta ke mata a gaban alkalin Kotun, tace ba gaskiya bane.

Bayan sauraron kowane ɓangare, Alkalin Kotun mai shari'a Labaran Gusau, ya sanar da ɗage zaman zuwa ranar 8 ga watan Nuwamba, 2022 domin dawowa a ci gaba da zaman shari'ar, NAN ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Naɗa Sabbin Kwamishinoni da Hadimai, Ya Yi Garambawul a Gwamnatinsa

Wata mata a Abuja na neman kyakkyawan namiji

A wani labarin na daban kuma Wata Hamshakiyar Mai Kudi a Abuja Na Neman Wanda Zai Dirka Mata Ciki, Zata Biya N3m

Wata Mai kuɗi dake zaune a Birnin tarayya Abuja ta shiga neman kyakkyawan Saurayin da zai iya ɗirka mata ciki.

Attajirar ta yi alkawari baiwa duk wanda iya wannan aiki kuɗi naira Miliyan Uku amma akwai sharuddan da ta kafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel