Shugaban Hukumar INEC Ya Rantsar da Sabbin Kwamishanoni 19, Jerinsu

Shugaban Hukumar INEC Ya Rantsar da Sabbin Kwamishanoni 19, Jerinsu

  • Daga karshe, an rantsar da kwamishanonin da zasu jagorancin gudanar da zaben badi 2023
  • Daga cikin mutum 19 da aka rantsar, akwai mutum biyar da sake nadasu akayi yayinda sauran sabbi ne
  • An yi zargin cewa wasu daga cikin wadannan kwamishanoni mambobin jam'iyyar APC ne

Abuja - Shugaban hukumar gudanar da zaben kasa mai zaman kanta watau INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, a ranar Alhamis ya rantsar da sabbin kwamishanonin hukumar REC guda 19.

An gudanar da bikin rantsar da su ne a hedkwatar hukumar dake birnin tarayya Abuja, rahoton ChannelsTV.

Farfesa Mahmoud a bikin ya yi kira da sabbin kwamishanonin su tabbatar da gaskiya a bakin aikinsu dake zuwa a zaben 2023.

Ba tare da bata lokaci ba ya tura kwamishanonin yankunan da zasu yi aiki.

A dokar hukumar, bai hallata a tura kwamishana jihar da mahaifarsa take ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

Mahmud Yakubu
Shugaban Hukumar INEC Ya Rantsar da Sabbin Kwamishanoni 19, Jerinsu Hoto: INEC
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerin kwamishanonin:

Ibrahim Abdullahi (Jihar Adamawa)

Obo Effanga ( Jihar Cross River)

Umar Ibrahim (Jihar Taraba)

Agboke Olaleke (Jihar Ogun)

Samuel Egwu (Jihar Kogi)

Onyeka Ugochi (Jihar Imo)

Muhammad Bashir (Jihar Sokoto)

Ayobami Salami (Jihar Oyo)

Zango Abdu (Jihar Katsina)

Queen Elizabeth Agwu (Jihar Ebonyi)

Agundu Tersoo (Jihar Benue).

Yomere Oritsemlebi (Jihar Delta)

Yahaya Ibrahim (Jihar Kaduna)

Nura Ali (Jihar Kano)

Agu Uchenna (Jihar Enugu)

Ahmed Garki (Jihar FCT)

Hudu Yunusa (Jihar Bauchi)

Uzochukwu Chijioke (Jihar Anambra)

Mohammed Nura (Jihar Yobe).

An zargi wasu cikin yan jam'iyyar APC ne

Legit.ng ta tattaro cewa wasu kungiyoyin sa kai sun tuhumci wasu daga cikin wadannan mutum 19 da alaka da wasu jam'iyyun siyasa.

Sun ce Muhammad Bashir, dan jihar Sokoto ya yi takarar gwamnan karkashin APC a 2015.

Hakazalika Sylvia Agu, yar jihar Enugu ana zargin kanwar mataimakin shugaban jam'iyyar APC ne na yankin kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC Ta Saki Jadawalin Yakin Neman Zabenta Na Shugaban Kasa

Kungiyar tace Pauline Onyeka, a baya an tuhumceta da rashawa tare da hadin kai da yan siyasa wajen magudin zabe.

Dalilin da yasa aka amince da su duk da zarge-zargen

Shugaban kwamtin majalisa kan INEC, Kabiry Gaya, ya tabbatar da cewa lallai an zargi wasu mutane cikin wadanda Buhari ya aike sunayensu, rahoton ThisDay.

Amma yace lokacin tantancesu, ba'a samu wani kwakkwarin hujjan dake nuna cewa suna da alaka da jam'iyyun siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel