Na Rantse Ina Da Ikon Hana Mutum Takara A PDP, Ayu Ya yiwa Ortom Hannunka Mai Sanda

Na Rantse Ina Da Ikon Hana Mutum Takara A PDP, Ayu Ya yiwa Ortom Hannunka Mai Sanda

Benue - Da alamun rikicin dake tsakanin shugaban uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party, Senator Iyorchia Ayu da Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, bai yi sauki ba.

Ayu ya ranste yana da karfin hana Ortom hawa kujerar Sanatan da yake takara karkashin jam'iyyar PDP.

Ortom da Ayu duka yan yanki daya ne a jihar Benue kuma sun yi hannun riga tun bayan zaben fidda gwanin dan takaran shugaban kasar jam'iyyar.

Ortom, da sauran takwarorinsa gwamnoni na Rivers, Oyo, Abia da Enugu sun bukaci Iyorchia Ayu yayi murabus saboda a samu zaman lafiya a jam'iyyar.

Ortom
Na Rantse Ina Da Ikon Hana Mutum Takara A PDP, Ayu Ya yiwa Ortom Hannunka Mai Sanda Hoto: Ayu/Ortom
Asali: Facebook

Yayin jawabi ga al'ummar garinsa a Gboko ranar Juma'a, Iyorchia Ayu wanda yayi magana a yarensa na 'Tibi' ya ce yana da ikon hana mutum takara karkashin tutar jam'iyyar musamman masu sukarsa a jihar, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Dan a mutun Peter Obi ya samu lambar yabo a kasar Tanzania bayan kafa tura a Kilimanjaro

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace amma a matsayin na uban kowa, ya hakura kuma ya yafe musu kuma yayi shiru kan lamarin.

Yace:

"Na yi shiru ka dukkan labaran da kuke ji a kaina saboda ban son kawo rabuwar kai cikin jam'iyyata a jihata, ina da karfi da ikon cewa mutum ba zai yi takara ba kuma ba zaka yi ba saboda sai na rattafa hannu za ka iya."
"Amma na sa hannu ga dukkan yan takaran PDP kuma kow aya tafi da halinsa, duk da bana so."
"Na yi hakan ne saboda ban son in cutar da kaina. Ina son jihar Benue ta lashe dukkan kuri'u saboda ace shugaban uwar jam'iyya ya bada kashi 90 na kuri'un jiharsa ga Alhaji Atiku Abubakar da kuma Titus Uba matsyain gwamna a 2023."

Asali: Legit.ng

Online view pixel