Jerin Abubuwa 7 Da Ka Iya Faruwa Da Mutum Idan Ya Ziyarci Jihohin Najeriyan Nan 14: Amurka

Jerin Abubuwa 7 Da Ka Iya Faruwa Da Mutum Idan Ya Ziyarci Jihohin Najeriyan Nan 14: Amurka

Gwamnatin kasar Amurka ta lissafo irin ayyukan laifi bakwai da ake aikatawa a Najeriya kuma ta gargadi yan kasarta su guji wasu jihohi 14 kada wadannan abubuwa su afka da su.

Wannan ya biyo bayan fitar da gargadin kai harin ta'addanci, wani sabon rahoto ya ce Amurka ta bada shawarwari ga yan Najeriya don kare kansu.

Gwamnatin ta Amurka ta gargadi yan kasarta mazauna Najeriya su guji wasu jihohin Najeriya saboda ana aikata wasu laifuka 7 a jihohin.

Biden
Jerin Abubuwa 7 Da Ka Iya Faruwa Da Mutum Idan Ya Ziyarci Jihohin Najeriyan Nan 14: Amurka
Asali: UGC

A jawabin da ofishin jakadancin Amurka ta fitar, ta bayyana cewa:

"Kada kuje jihohi kamar haka:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

  • Abuja saboda ta'addanci
  • Borno, Yobe, Kogi, da Arewacin Adamawa saboda yan ta'adda da garkuwa da mutane
  • Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano, Katsina, da Zamfara saboda garkuwa da mutane
  • Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Delta, da Rivers (Illa birnin Port Harcourt) saboda laifuka iri-iri, garkuwa da mutane, barayin cikin teku

Kara karanta wannan

An samu karin kasashe da suka gano yiwuwar kai hare-hare a Abuja da Jihohi 22

Ana aikata laifuka irinsu:

  • fashi da makami,
  • yan bindiga dadi,
  • kwacen mota,
  • garkuwa da mutane don karban fansa,
  • sace mutum don wata manufa daban,
  • hare-haren yan bindiga
  • fyade

Jawabin ya kara da cewa:

"Ana yawan garkuwa da mutane don karban fansa sosai, musamman yan Najeriyan da suka kawo ziyara daga kasar waje, da kuma yan kasar Amurka da akewa kallon suna da kudi."
"Kungiyoyin yan bindiga na tare hanyoyin jiha da jiha."

Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

Hukumar tsaron farin kaya DSS, hukumar leken asirin Najeriya NIA, yan sanda da sauran jami'an tsaro sun kai harin kwantan bauna kauyukan Abuja kuma sun yi babban kamu.

Punch ta ruwaito cewa jami'an tsaron sun garkame kwamandojin ISWAP biyar da mayaka 30 a unguwanni irinsu Mararaba dake makwabtaka da ke kwaryar birnin tarayya Abuja.

Rahoton ya kara da cewa suna tsare yanzu a ofishin DSS.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

An tattaro cewa hukumomin tsaron sun kwana biyu suna bibiyan yan ta'addan gabanin gargadin da Amurka da Birtaniya sukayi ranar Lahadi na cewa yan kasarsu suyi hattara da Abuja.

Wata majiyar tsaro da tayi karin haske kan lamarin tace yan ta'addan na shirin kai munanan hare-hare Abuja kafin aka kamasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel