Shugaba Muhammadu Buhari Zai Shilla Kasar Koriya Ta Kudu Gobe

Shugaba Muhammadu Buhari Zai Shilla Kasar Koriya Ta Kudu Gobe

  • Shugaba Buhari zai tashi daga Abuja gobe Lahadi zuwa nahiyar Asiya don halartan taro kiwon lafiya
  • Wannan shine karo na farko da kungiyar lafiya ta duniya da gwamnatin Koriya ke shirya wannan taro
  • Shugba Buhari zai samu rakiyar wasu daga cikin mukarrabansa don halartan taron na kwana biyu

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Koriya ta kudu, nahiyar Asiya a gobe Lahadi, 23 ga watan Oktoba 2022.

Buhari zai dira birnin Seoul ne domin halartan taron ilmin hallita da rigakafi na duniya.

Wannan shine karin farko da za'a shirya wannan taro.

Hadimin shugaba Buhari kam lamarin sadarwan zamani, Bashir Ahmed, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

A cewarsa, Buhari zai gabatar da jawabi a taron da aka shirya ranar 25 da 26 ga Oktoba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kasar Dubai Ta Dakatad Da Baiwa Yan Najeriya Biza Gaba Daya

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shugaba Buhari gobe zai bar Abuja don zuwa Seoul, koriya ta kudu domin halartan taron ilmin halitta na duniya karon farko da gwamnatin Koriya da kungiyar lafiyan duniya ta shirya."
"Taron na kwana biyu (October 25-26), mai take "Rana goben rigakafi da ilmin halitta."

Kayi Zamanka a Najeriya, Kada Ya Zo Yanzu: Gwamnatin Qatar Ga Shugaba Buhari

A watan jiya, Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin kasar Qatar ta dakatad da zuwan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kasarta yayinda yake shirin zuwa kasar ta Larabawa.

Gwamnatin Qatar musamman ta bukaci a dage tafiyar da aka shirya yi watan Satumban nan.

TheCable ta ruwaito cewa ofishin jakadancin Qatar a wasikar da ta aikewa ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ranar 19 ga Agusta yace ranar da Buhari ke shirin zuwa ba zai yiwu ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Buhari ya kaddamar da kwamitin da zai tallata Tinubu a Najeriya

An shirya Shugaba Buhari zai tafi Qatar ranar 11 ga Satumba, 2022 bisa gayyatar Sarkin Qatar Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani.

A cewar wasikar:

"Ofishin jakadancin kasar Qatar dake Abuja gaisuwa ga ma'aikatar harkokin wajne Najeriya musamman kan wasikar sanar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da zuwa kasar Qatar ranar 11-12 Satumba 2022 bisa gayyatar Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani, Sarkin Qatar.

"Amma Wannan rana da aka shirya zuwa ba zai yiwu ba saboda haka muna bukatar Najeriya ta zabi wata rana cikin rubu'in farko na shekarar 2023."

Ana hasashen wannan wasika bai rasa alaka da gasar kwallon duniya da aka shirya bugawa a Qatar 2022 daga ranar 21 ga Nuwamba zuwa 18 ga Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel