Gwamnatin Kasar Dubai Ta Dakatad Da Baiwa Yan Najeriya Biza Gaba Daya

Gwamnatin Kasar Dubai Ta Dakatad Da Baiwa Yan Najeriya Biza Gaba Daya

  • Daga Yanzu Gwamnatin kasar Dubai Ta Daina Ba Duk Wani Dan Najeriya Bizan zuwa Kasar
  • Daga yanzu duk dan Najeriyan da ke son bizan zuwa shakatawa Dubai yayi hakuri har sai wani lokaci
  • Da Farko Masu Kasa Da Shekaru 40 kadai aka daina baiwa Bizan zuwa Dubai amma yanzu ta shafi kowa

Hukumomi a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a ranar Juma'a ta yanke shawarar haramtawa yan Najeriya Biza shiga birnin Dubai gaba daya.

A wasikar sanarwar da gwamnatin ta yiwa abokan hukdanta irinsu kamfanonin jirage da dillalan tafiya, gwamnatin kasar ta ce daga yanzu duk wanda ya nemi biza ba za'a bashi ba, rahoton Tribune.

A cewar wasikar:

"Wannan sabuwar doka ta shafi dukkan yan Najeriya a wannan lokaci."

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Tinubu ya yi magana mai girma game da bashin da ake bin Najeriya

"Ku baiwa kwastamominku shawara su sake bada takardar C2=AO idan aka sulhunta tsakanin Gwamnatin Najeriya da Na mu."

Har yanzu dai basu bayyana takamammen dalilin yin haka ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dubai ya kasance daya daga cikin garuruwan da yan Najeriya ke zuwa don yawon bude ido, shakatawa, da kasuwanci.

Dubai
Gwamnatin Kasar Dubai Ta Dakatad Da Baiwa Yan Najeriya Biza Gaba Daya Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Da farko, Sakamakon rikicin da yan Najeriya ke yi a Dubai, gwamnatin hadaddiyar daular Larabawa (UAE) ta gindaya sabbin sharruda wa yan Najeriya.

Rahotanni sun nuna yadda wasu yan Afrika da ake zargin yan Najeriya ne ke haddasa rikici a kasar Dubai kuma an fitittiki da dama cikinsu.

Shugabar hukuma yan Najeriya mazauna kasashen waje ya zayyana jerin sharrudan da gwamnatin UAE ta gindaya yanzu.

A cewarta, ba za'a baiwa dan Najeriya Biza ba sai ya cika wadannan sharruda.

Ga jerinsu:

Kara karanta wannan

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Ya Angwance Da Gwanar Al-Qur'ani Hafiza Haulatu

1. Dole sai ka kasace mai shekaru akalla 40

2. Dan kasa da shekaru 40 sai da ya tafi da iyalinsa, za'a bashi 'Family Visa'

3. Sai ka nuna hujjan cewa ka kama Otal ko wani wajen zama a UAE

4. Zai ga gabatar da takardan hada-hadan bankin na watanni 6 (Bank account Statement)

5. Sai ka nuna cewa ka sayi tikitin dawowa Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel