Kayi Zamanka a Najeriya, Kada Ya Zo Yanzu: Gwamnatin Qatar Ga Shugaba Buhari

Kayi Zamanka a Najeriya, Kada Ya Zo Yanzu: Gwamnatin Qatar Ga Shugaba Buhari

  • Gwamnatin Qatar ta bayyanawa Shugaba Muhammadu Buhari cewa kada ya zo kasarsu wannan shekarar
  • Zaku tuna cewa Sarkin Kasar Qatar, Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani, ya gayyaci Shugaba Buhari kasar
  • Amma ana kyautata zaton gwamnatin ta dage zuwan Buhari bisa gasar kwallon kafan duniya da za'ayi a kasar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin kasar Qatar ta dakatad da zuwan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kasarta yayinda yake shirin zuwa kasar ta Larabawa.

Gwamnatin Qatar musamman ta bukaci a dage tafiyar da aka shirya yi watan Satumban nan.

TheCable ta ruwaito cewa ofishin jakadancin Qatar a wasikar da ta aikewa ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ranar 19 ga Agusta yace ranar da Buhari ke shirin zuwa ba zai yiwu ba.

An shirya Shugaba Buhari zai tafi Qatar ranar 11 ga Satumba, 2022 bisa gayyatar Sarkin Qatar Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban CAN ya magantu kan abin da ya kamata fastoci su yi a lamarin jam'iyya

Buhari
Kayi Zamanka a Najeriya, Kada Ya Zo Yanzu: Gwamnatin Qatar Ga Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wasikar:

"Ofishin jakadancin kasar Qatar dake Abuja gaisuwa ga ma'aikatar harkokin wajne Najeriya musamman kan wasikar sanar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da zuwa kasar Qatar ranar 11-12 Satumba 2022 bisa gayyatar Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani, Sarkin Qatar.
"Amma Wannan rana da aka shirya zuwa ba zai yiwu ba saboda haka muna bukatar Najeriya ta zabi wata rana cikin rubu'in farko na shekarar 2023."

Ana hasashen wannan wasika bai rasa alaka da gasar kwallon duniya da aka shirya bugawa a Qatar 2022 daga ranar 21 ga Nuwamba zuwa 18 ga Disamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel