UI, UNILAG, BUK da Wasu Manyan Jami'o'i 7 da Za Ku Iya karanta Ilimin Shari'a a Najeriya

UI, UNILAG, BUK da Wasu Manyan Jami'o'i 7 da Za Ku Iya karanta Ilimin Shari'a a Najeriya

Jami'ar Ibadan (UI) ta fito ta daya a jerin jami'o'i mafi nagarta a Najeriya ga duk wanda ke son karanta fannin shari'a a kasar nan, a cewar rahoton Times Higher Education World University dake duba nagartar jami'o'i.

A rahoton na 2023, Jami'ar Legas (UNILAG) ta fito a jerin da UI ta fito na nagartattun jami'oi.

Dukkansu biyu, UI da UNILAG sun fito ne tsakanin matsayin 401-500 a cikin jami'o'in duniya sama da 1,799.

Jerin jami'o'in Najeriya da za ku iya karanta ilimin shari'a
UI, UNILAG, BUK da Wasu Manyan Jami'o'i 7 da Za Ku Iya karanta Ilimin Shari'a a Najeriya | Hoto: AMINU ABUBAKAR/AFP
Asali: Getty Images

Da ta fito a tsakanin 1001 da 1200, jami'ar Bayero ta Kano ne ta uku a jerin jami'o'i masu nagarta wajen karanta fannin shari'a a Najeriya.

The Times Higher Education, wata mujallace ta kasar Burtaniya da ta kware wajen gwada matsayin jami'o'i a duniya.

Kara karanta wannan

Saura Yan Watanni Ya Sauka: Lokuta 5 Da Wike Nade-Nade Mutum 100,000 Don Tsare Akwatin Zabe A 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nagartattun jami'o'i 10 da za ku karanta fannin shari'a a Najeriya

A kasa, mun kawo muku jerin jami'o'i 10 da za ku iya bibiya don karanta fannin shari'a, kamar yadda yazo a rahoton na THE a 2023

LambaJami'o'in NajeriyaMatsayi a NajeriyaMatsayi a duniya
1Jami'ar Ibadar (UI)1401-500
2Jami'ar Legas (UNILAG)1401-500
3Jami'ar Bayero ta Kano (BUK)31001-1200
4Jami'ar Benin (UNIBEN)41201-1500
5Jami'ar Ilorin (UNILORIN)41201-1500
6Jami'ar Najeriya ta Nsukka (UNN)41201-1500
7Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU)41201-1500
8Jami'ar Nnamdi Azikwe (UNIZIK)81501+
9Jami'ar Jiha ta Adamawa, Mubi9"Akwai bayani"
10Jami'ar Tarayya ta Alex Ekwueme, Ndufu-Alike9"Akwai Bayani"

Tambihi: Jami'ar Jiha ta Adamawa dake Mubi da Jami'ar Tarayya ta Alex Ekwueme dake Ndufu Alike basu samu lambar matsayi ba.

Kara karanta wannan

Jerin Kasashen Duniya 10 Mafi Adadin Rundunar Soja a Duniya a 2022

Abin da hakan ke nufi, jami'o'in biyu suna daga jami'o'i 526 da aka duba nagartarsu a duniya.

Sun gabatar da takardun tantance jami'a, amma basu cika ka'idojin da ake bukata ba. Sai dai, sun amince a bayyana su a jerin jami'o'in da ake da rahotonsu a hannu.

Babban Abin da Ya sa Muka Hakura, Muka bude Jami’o’i Bayan Wata 8 inji ASUU

A wani labarin, shugaban kungiyar ASUU ta malaman jami’a, Emmanuel Osodeke yace hukuncin kotu ne babban abin da ya tursasa masu komawa bakin aiki.

The Cable ta rahoto Farfesa Emmanuel Osodeke yana mai cewa malamai sun janye yajin-aikin da su ke yi ne saboda Alkali ya umarci su bude makarantu.

Kungiyar ASUU tace duk da an janye yajin-aikin bayan watanni takwas, har yanzu ba ta cin ma matsaya da gwamnatin tarayya kan wasu batutuwan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel