Ana Saura Yan Watanni Ya Sauka: Yadda Wike Yayi Nade-Nade Don Tsare Akwatin Zabe A 2023

Ana Saura Yan Watanni Ya Sauka: Yadda Wike Yayi Nade-Nade Don Tsare Akwatin Zabe A 2023

Ana saura watanni takwas karewar wa'adin mulkinsa matsayin gwamna, Nyesom Wike na Rivers ya yi manyan nade-nade na dubunnan mutane lokaci guda.

Wannan ya biyo bayan rikice-rikicen da ke gudana tsakanin gwamnan da uwar jam'iyyarsa ta Peoples Democratic Party PDP.

A cikin wata guda kadai, Wike ya nada mutum kimanin dubu saba'in don kare muradun zaben da za'ayi a 2023.

A mukaman da ya bada, Wike ya sanya mutane a kowani lungu da sakon jihar don tsare masa akwatin zaben jiharsa gaba daya.

Bayan wadannan nade-nade, Wike dai ya bayyana cewa muddin ya raba jiha da jam'iyyar PDP babu yadda za'a yi ta lashe zabe.

Nyesom Wike
Ana Saura Yan Watanni Ya Sauka: Yadda Wike Yayi Nade-Nade Don Tsare Akwatin Zabe A 2023
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit ta tattaro muku jerin nade-naden da Wike yayi:

1. Nadin mutum 40 matsayin Jami'an Lura na kananan hukumomi

A ranar 11 ga Oktoba, Wike ya nada mutum 40 matsayin wakilai na kananan hukumomi

2. Nadin mutum 319 matsayin Jami'an Lura na gundumomi

Hakazalika a wannan rana, Wike ya nada mutum 319 da zasu lura da kuri'u a gundunomin jihar 319.

3. Nadin masu bashi shawara na musamman na akwatinan zabe 14,359

Ba tare da bata lokaci ba, Wike ya kara nada mutum 14,359 matsayin wadanda zasu lura masa da akwatinan zabe sama da 14,000 dake fadin jihar.

4. Nadin hadimai na musamman guda 50,000

Yayinda aka fara cece-kuce kan nadin, Wike ya kara bada mamaki inda ya sanar da nadin mutum 50,000 matsayin wadanda zasu bashi shawara kan rumfuna da akwatunan zabe a 2023.

5. Fadada Nadin hadimai na musamman zuwa 100,000

Wike a ranar Juma'a, 14 ga Oktoba ya fadada nadin hadiman zuwa 100,000.

Ya bayyana hakan ne yayin zaman da yayi da yan jarida a gidan gwamnatin jihar.

Ya bayyana cewa ya cika dukkan alkawuransa na ayyukan ganin da ido tare da matsawa zuwa gina jama'a a fannin siyasar jihar tasa.

Babu Yadda Atiku Da PDP Zasu CI Zabe Idan Na Fita Daga Jam'iyyar

Wike, ya bayyana cewa idan ya fita daga jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) yau, babu yadda za'ayi su ci zabe a 2023.

Wike ya bayyana hakan ne yayin hira da yan jarida ranar Juma'a a garin Port Harcourt, babbar birnin jihar.

Yace irin karfin da shi da abokansa ke da shi babu wanda ya isa ya raina su kuma jam'iyyar PDP na bukatarsu idan tana son nasara a 2023.

Wike ya lashi takobin cewa sai shugaban uwar jam'iyyar, Iyorchia Ayu, ya yi murabus daga kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel