Jerin Kasashen Duniya 10 Mafi Adadin Rundunar Soja a Duniya a 2022

Jerin Kasashen Duniya 10 Mafi Adadin Rundunar Soja a Duniya a 2022

  • Kowace kasa na alfahari da adadin Sojojin da take shi da makamai irinsu bindigogi, tankoki da sauransu
  • Yayinda wasu ke tunanin Amurka ta fi kowa karfi, kasar Sin ta zarce mata wata adadin runduna
  • Kasashen da ke da makamar nukiliya ake ganin sun fi hadari a yanzu

Wani jerin kasashe masu karfin Soja a duniya a 2022 da Statista ta saki ya nuna cewa kasar Sin ne kan kan gaba wajen yawan jami'an sojoji, rahoton Statista ta bayyana.

Rahoton ya nuna cewa kasar sin na adadin Sojoji milyan 2.19 dake shirye da fuskantar yaki. Kasar da ta samu damar zuwa ta biyu itace Indiya mai adadin Sojoji milyan 1.45.

Amurka ce ta zo na uku da Sojoji milyan 1.4, sannan sai kasar Koriya ta Arewa.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Haramtawa EFCC Kwace Wasu Manyan Kadarorin Gwamna Matawalle

Ga jerin kasashe 10 mafi karfin Soja a duniya:

1. Sin: 2,000,000

2. Indiya: 1,450,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

3. Amurka: 1,390,000

4. Korea ta Arewa : 1,200,000

5. Rasha: 850,000

6. Pakistan: 640,000

7. Iran: 575,000

8. Korea ta kudu: 555,000

Photo CreditL Statista
Jerin Kasashen Duniya 10 Mafi Adadin Rundunar Soja a Duniya a 2022 Photo Credit: Statista
Asali: UGC

Legit.ng ta lura cewa kasar Afrika daya kacal cikin manyan kasashe 10 mafi karfin Soja.

Amma a 2019, Sojojin Najeriya sun zo na hudu a jerin Soji mafi karfi a nahiyar Afrika.

A bisa rahoton da Statista ya saki, Najeriya ta biyo bayan Misra, Aljeriya, da Afrika ta kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel