Kasafin Kuɗin 2023: An Ware N1.6bn Don Ciyar da Daliban Firamare Da TraderMoni

Kasafin Kuɗin 2023: An Ware N1.6bn Don Ciyar da Daliban Firamare Da TraderMoni

  • Ana ci gaba da bayyana kowanne ɓangare na ma'aikatun gwamnati adadin da zasu samu a kasafin kuɗin 2023
  • Daga ciki harda tsarin da ke kula da ciyar ƴan makarantun Firamare da kuma tallafawa masu ƙananan kasuwanci
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2023 na sama da Naira Tiriliyan 20

Abuja - An ware Naira biliyan 1.6 don shirin ciyar da makarantun firamare da ƴan kasuwa dake da ƙaramin jari ko neman tallafi a cikin kasafin kuɗin shekarar 2023

Zaku tuna shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gabatar wa majalisar dokokin kasar a makon jiya a ranar Juma’a, Kamar yadda jaridar THE PUNCH ta rawaito

Ayyukan da aka bayyana a matsayin "sababbin", an sanya su ne a cikin kasafin kudin 2023 a ƙarkashin ofishin Ma'aikatar Agaji da Kula da jin Ƙai, bisa ga tsarin gwamnati na tallafawa masu karamin ƙarfi.

Kara karanta wannan

Kasafin Kuɗi 2023: Kudi N22.44Bn gwamnatin tarayya ke shirin kashewa yan gidajen yari

Duk da cewa hukumar ba ta fayyace adadin yaran da take son ciyarwa ba da ma wadanda za'a tallafawa daga cikin masu ƙananan sana'oin ba, amma an lura cewa ayyukan na daga cikin manyan ayyukan hukumar da ke ƙunshe a cikin kasafin kudin shekarar 2023.

Dangane da ciyar da ƴan firamare kuwa, an ware naira biliyan 1, yayin da aka ware N600,000,000 dan masu ƙananan sana'oi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abinci
Kasafin Kuɗin 2023: An Ware N1.6bn Don Ciyar da Daliban Firamare Da TraderMoni
Asali: Original

Cece-kuce game da shirin ciyar da ƴan makarantu firamare da tallafawa masu ƙananan sana'oi.

Misali, a watan Oktoban 2022, gwamnatin jihar Nassarawa ta lura cewa ta bankado makarantun bogi 349 da aka sanya a cikin shirin da aka fitar da kudade.

A watan Yunin 2022, gwamnatin tarayya ta bayyana gazawarta na kwato kudaden tallafin da aka bawa masu ƙananan sana'oi da ya tasarma Naira biliyan 10 da aka fitar a kashin farko, bayan shekaru uku.

Kara karanta wannan

Jinkirin Karasa Layin Dogon Kaduna Zuwa Kano: Gwamnatin China Ta Hana Najeriya Bashi

Shi dai tsarin Tradermoni lamuni ne wanda ba shi da ruwa da ake bai wa ‘yan kasuwa, a karkashin shirin Kamfanonin Gwamnati da Karfafa musu gwiwa, wanda aka fara a shekarar 2018, jim kadan kafin babban zaben shekarar 2019.

Dala Miliyan 100 Muka Kashe Wajen Ciyar da Ɗalibai Miliyan 10, Gwamnatin Tarayya

A baya mun kawo muku cewa Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da kashe naira miliyan ɗari wajen ciyar da yara ɗalibai miliyan goma a ƙarƙashin Tsarin Ciyarwa Na Gwamnatin Tarayya.

Wannan wani shiri ne domin rage bautar da yara da ake a Najeriya da ƙarfafa wa iyaye kai ƴaƴansu makaranta.

Ministan Ma’aikata da Ayyuka na ƙasa, Sanata Chris Ngige, ne ya tabbatar da haka a ofishinsa da ke Abuja a yayin da yake karɓar baƙuncin Jakadan ƙasar Amurka a Najeriya, Mary Beth.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel