Jinkirin Ginin Layin Dogon Kaduna Zuwa Kano: China Ta Hana Najeriya Bashi

Jinkirin Ginin Layin Dogon Kaduna Zuwa Kano: China Ta Hana Najeriya Bashi

  • Gwamnatin Najeriya ta fito ta yi bayanin dalilin rashin ƙarasa layin dogon Kaduna zuwa Kano da bata yi ba
  • Gwamnatin tarayya dai ta tsara kammala waɗannan ayyuka na layin dogo ne kafin ƙarewar wa’adin mulkin shugaba Buhari
  • Sai dai abin da kamar wuya, idan aka yi la’akari da cewa Najeriya na jiran bashin da China za ta ba ta ne domin ƙarasa waɗannan ayyuka abin da bai gaza shekara guda ba

Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo, ya ce gwamnatin Najeriya na jiran ƙarin rancen kuɗaɗe ne daga ƙasar Sin domin ƙarasa ayyukanta na layin dogo.

Ayyukan layin dogon dai sun haɗa da: layin dogo na Abuja zuwa Kano da Fatakwal zuwa Maiduguri.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja, a ranar Juma’ar nan, cewa rashin ƙarasa aikin laukan dogon ya faru sakamakon rashin samun kaso 85 cikin ɗari na rancen da ta nema.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe $100m wajen ciyar da daliban makaranta 10m

BUhari
Jinkirin Ginin Layin Dogon Kaduna Zuwa Kano: China Ta Hana Najeriya Bashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rashin samun wannan rance, kamar yadda ministan ya bayyana da kuma amfani da wasu kuɗaɗe daga wasu ɓangarori ne ke cigaba da kawo tsaikon ƙarasa wannan ayyuka.

Yace:

“Muna cigaba da yin wannan aikin ne da kashi sha biyar na kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta shirya bayarwa domin kammala aikin wanda kuma ba zai isa a gani a ƙasa ba.”
Sannan ministan ya ɗora da cewa; “tabbas game da kashi sha biyar ɗin can na aikin layin dogo daga Abuja zuwa Kano, tabbas mun ba wa ƴan kwangilar kuɗaɗe,”.
“Kuma har sai mun sami wancan kaso tamanin da biyar ɗin ne, za mu iya kammala aikin. Amma za a cigaba da yin sa da wannan kuɗi da muka riga muka ware.”

Ƙasar Sin dai ita ce ta gaba-gaba wajen bin Najeriya bashi, inda take bin ta jimillar Dalar Amurka biliyan uku da dubu ɗari tara a bayanan da aka tattara na watan 30 ga Yuni, 2022.

Kara karanta wannan

Biden Ya Yafewa Dubban Yan Amurka, Yace Daga Yanzu Mallakar Wiwi Ba Laifi Bane

Sannan Legit.ng ta rawaito yadda buƙatar Buhari da ya gabatar wa da Majalisun ƙasar game da sake ciwo bashi ta tada hazo a tsakanin ƴan Najeriya.

Shugaban dai ya roƙi sahalewar majalisar domin karɓo bashin dala biliyan huɗu da miliyan hamsin da huɗu da wasu yuro miliyan goma da dala miliyan ɗari da ashirin da biyar.

Sai dai da yawan ƴan Najeriya na cigaba da nuna rashin amincewarsu da wannan rance da za a ciwo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel