Dala Miliyan 100 Muka Kashe Wajen Ciyar da Ɗalibai Miliyan 10, Gwamnatin Tarayya

Dala Miliyan 100 Muka Kashe Wajen Ciyar da Ɗalibai Miliyan 10, Gwamnatin Tarayya

  • Bautar da yara dai abu ne da Najeriya ke cigaba da fama da shi a kusan ko’ina a ƙasar
  • Sai dai Ministan Ma’aikata da Ayyuka, Ngige ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya tana ciyar da yara miliyan goma a makarantu daban-daban a Najeriya
  • Ya yi kira ga ƙasar Amurka da ta taimaka wa Ma’aikatarsa domin ganin an ceto yara da ake bautar tare da dawo da su zuwa makaranta da rage wa iyayensu talauci

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da kashe naira miliyan ɗari wajen ciyar da yara ɗalibai miliyan goma a ƙarƙashin Tsarin Ciyarwa Na Gwamnatin Tarayya.

Wannan wani shiri ne domin rage bautar da yara da ake a Najeriya da ƙarfafa wa iyaye kai ƴaƴansu makaranta.

Ministan Ma’aikata da Ayyuka na ƙasa, Sanata Chris Ngige, ne ya tabbatar da haka a ofishinsa da ke Abuja a yayin da yake karɓar baƙuncin Jakadan ƙasar Amurka a Najeriya, Mary Beth.

Wannan jakada ya samu rakiyar wasu jami’an biyu daga ofishin na jakadancin Amurka.

Ngige
Dala Miliyan 100 Muka Kashe Wajen Ciyar da Ɗalibai Miliyan 10, Gwamnatin Tarayya
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ngige ya ƙara yin fashin baƙi game da manufar gwamnati, inda ya bayyana cewa an ƙirƙire shi ne domin jan hankalin yara da suke aiktau wajen dawowa makaranta.

Sannan gwamnatin tarayya ta ƙirƙiri shirin domin rage talauci wanda hakan ke jawo yara su tsinci kansu a cikin wannan hali na bautarwa da sauransu.

A wani jawabi da mai mai magana da yawun ma’aikatar ta Ma’aikata da Ayyuka, Olajide Oshundun, ya fitar, an ji yadda Ngige yake cewa;

“Mun kawo wannan tsari na ciyarwa a makarantu ne domin jan ra’ayin yara kan yin sha’awar zuwa makaranta, inda muke ciyar da yara har miliyan goma a faɗin ƙasar wanda kuma muka kashe dalar Amurka miliyan goma.”
“Sannan mun fi zaɓar makarantu a wuraren da muke ganin an fi fuskantar bautar da yara tare da yin karatu kyauta ta hanyar dokar samar da Ilimi ta Baiɗaya da ƴancin Yara.,” a cewar Ngige.

“Game da mutane masu larura ta musamman, mun ƙirƙiri Hukumar Masu Lurara Ta Musamman domin samar musu da gamsasshen taimako saboda cire musu jin cewa suna da wata naƙasa.
Saboda idan ba a taimaka wa masu larura ta musamman ba, to kai tsaye hakan zai jefa su a cikin wani mawuyacin hali,” Ngige ya tabbatar.

Sannan ya cigaba da cewa ko a makon da ya wuce, an ware dalar Amurka miliyan goma domin yaƙi da bautar da yara a Najeriya.

Kuma an zaɓi jihar Ondo domin bunƙasa noman bishiyar koko (Cocoa) wanda wannan mataki ne mai muhimmanci, domin a taruka da dama da muka halarta, mun fito da muhimmancin yin hakan,” a cewar Ngige.

Ya tabbatar da cewa yawan faɗar matsalar da yara ke fuskanta ba zai magance komai ba, inda ya buƙaci cewa lallai ne gwamnatin Amurka ta taimaka wa Najeriya domin yaƙar matsalar bautar da yara da ake yi.

Jakadiyar ta Amurka ta ce Amurka ba ta jin daɗin game da yadda ake bautar da yara a wuraren haƙo ma’adanai da sauransu.

Ta kuma tabbatar da cewa Amurka za ta cigaba da haɗa kai da Najeriya wajen magance wannan matsalar. Ta kuwa yi kira ga jihohi bakwai na ƙasar nan da su tabbatar da dokar ƴancin yara a jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel