Biden Ya Yafewa Dubban Yan Amurka, Yace Daga Yanzu Mallakar Wiwi Ba Laifi Bane

Biden Ya Yafewa Dubban Yan Amurka, Yace Daga Yanzu Mallakar Wiwi Ba Laifi Bane

  • Shugaban Amurka, Joe Biden, ya ce dagayanzu ba laifi ba ne sarrafa wiwi domin yin magani
  • Wannan ta sa ya yafe wa dubun nan ɗaurarru a Amurka da aka kama suna ta’ammali da wiwi
  • Yayi kira ga sauran gwamnoni kasar su yi koyi da shi tare da umartar wasu hukumomi biyu da su sake nazarin dokar haramta amfani da wiwi

Shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden, ya bayyana cewa ba laifi ba ne sarrafa wiwi domin samar da magani.

Ya bayyana hakan ne ta shafin Twitter a wani yunƙuri na cika wa magoya bayansa alƙawarin da ya yi na rage kallon hadarin kaji da ake yi Wawi a matsayin magani.

Wannan na zuwa ne wata ɗaya gabanin zaɓen da ke tunkararsu, inda shugaban ƙasar ya yi wa dubun nan ƴan ƙasar da ke tsari afuwa da aka kama saboda ta’ammali da wiwi.

Kara karanta wannan

Lokacin Da Na Hau Mulki Kukan Tashin Bama-Bamai Yan Najeriya Ke Yi, Buhari

Sannan ya umarci hukumomin lafiya da na shari’a da su sake duba matsayin wiwi ɗin, domin ganin ko za a iya sa ta cikin sinadarai marasa haɗari sosai.

Biden
Biden Ya Yafewa Dubban Yan Amurka, Yace Daga Yanzu Mallakar Wiwi Ba Laifi Bane
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu masu faɗa a ji na ƙasar ta Amurka sun bayyana cewa kusan mutane dubu shida da ɗari biyar ke fuskantar tuhuma game da ta’ammali da wiwi.

Sannan hukumomin ƙasar sun ƙara tabbatar da cewa akwai yiwuwar yi wa wasu dubun nan makamanciyar wannan afuwa.

Sai dai wannan yunƙuri na shugaba Joe Biden wani mataki ne na jan hankali ko tursasa wa hukumomi a ko’ina suke domin su yi koyi da shi.

Yace:

“Ina jan hankalin gwamnonin ƙasar nan tawa da su kwaikwayi ni ta fuskar kundin laifuffuka na ƙasa, domin bai kamata mutum ya kasance a gidan yari na jiha saboda akwai an same shi da wiwi ba,”.

Kara karanta wannan

Sai Na Magance Matsalar Tsaro Kafin Na Sauka Daga Mulki, Shugaba Buhari

“Rayuka da yawa sun shiga wani hali saboda yadda muke kallon wasu al’amura. Don haka ina sanar da yafe wa waɗanda aka riga aka kama da wiwi.”

Sai dai hakan ba yana nuna amincewarsa ba ne ga janye dokar haramcin taƙaita fasaƙwaurinta ba ne ko kasuwancinta ko kuma sayar wa da ƙananan yara ƙasa da shekaru 18.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel