Fashewar Bama-Bamai: Kukan Daɗi Ƴan Najeriya Ke Yi a Yanzu, In ji Buhari

Fashewar Bama-Bamai: Kukan Daɗi Ƴan Najeriya Ke Yi a Yanzu, In ji Buhari

  • Shugaba Buhari ya tuna wa Najeriya irin haɗin da ya samu ƙasar nan a ciki lokacin da ya hau mulki
  • Ya bayyana cewa bama-bamai ne ke fashewa ko’ina kuma gwamnatinsa ce ta magance hakan.
  • Sannan ya bayyana irin nasarori da ya samu ta fuskar samar da kayan aiki ga sojin Najeriya

Kaduna - Shugaba Muhammadu Buhari ya kwarzanta cewa gwamnatinsa ta yi nasarar rage matsalar tsaro a Najeriya, idan aka yi la’akari da irin yadda ya samu ƙasar.

Shugaban ya bayyana cewa, ya samu ƙasar ne a lokacin da ake ruwan bama-bamai a kusan kowanne lokaci har a biranenmu.

Shugaba Buhari na faɗin hakan ne a yayin taron yaye jami’an soji da suka kammala karɓar horo a ranar Alhamis ɗin a makarantar horar da sojoji (NDA) da ke Kaduna, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Sai Na Magance Matsalar Tsaro Kafin Na Sauka Daga Mulki, Shugaba Buhari

Buhari NDA
Fashewar Bama-Bamai: Kukan Daɗi Ƴan Najeriya Ke Yi a Yanzu, In ji Buhari Hoto: BUhari

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta cigaba da samar da kayan aiki ga rundunar sojojin domin magance ta’addanci a ƙasar baki ɗaya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sannan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa ta inganta kasafin kuɗin da suke ba wa manyan jami’an sojin ƙasar nan.

A cewarsa:

“A lokacin da muka karɓi mulki a 2015, mun tarar da ƙasar tana fama da bama-bamai a ko’ina; har ma da cikin birane. Amma mu ne muka magance hakan” .
“Mun bunƙasa ɓangaren sojin ruwa tare da kuma ƙara adadin jami’an sojin sama da kaso 38 cikin ɗari da kuma inganta lafiyar jiragen sashen da kashi 70 cikin ɗari.
Sannan mun samar da motocin yaƙi har guda ɗari biyu da bindigu da sauran kayan aiki wanda hakan ƙari ne kawai ga irin inganta kuɗaɗen da muke ba wa rundunar da sauran jami’an fikira,”

Kara karanta wannan

An damke Soja yana baiwa masu garkuwa da mutane hayar bindiga AK-47

Sannan shugaban ya cigaba da cewa wannan yunƙuri nasu na samar da kayyayakin nan a cikin shekaru 7 manuni ne na irin alƙawarin da suka yi na inganta ɓangaren tsaro na ƙasar nan.

Don haka ya buƙace su da dagewa wajen kiyaye tattalin arziƙi da tsaron ƙasar nan, domin ka da a zuba ido ‘yan ta’adda su ruguje nasarorin da gwamnatin ta samu.

“Wannan abu ne mai muhimmanci a gare mu, domin burinmu shi ne miƙa wa gwamnati mai zuwa ƙasa dake zaman lafiya da kuma ingantancen tsaro a matsayin abin tunawa ga al’umma,” a cewar Buharin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel