An Ceto Jaririn Da Wata Mata Ta Sace A Asibitin ATBU Bauchi

An Ceto Jaririn Da Wata Mata Ta Sace A Asibitin ATBU Bauchi

  • Jami'an tsaro sun ceto yaro daya daga cikin tagwayen da wata mata ta sace a asibitin ATBU a Bauchi
  • Makon da ya gabata wata mata ta sace jinjirin yayinda tayi shigar ma'aikatan asibitin sannan ta bukaci mika jinjirin sashen shan magani
  • An damke wacce ake zargi da sace jaririn kuma an kaddamar da bincike kan lamarin

Hukumomin asibitin koyarwan jami'ar Abubakar Tafawa Balewa ATBUTH dake jihar Bauchi sun bayyana cewa an gano dan tagwayen da aka sace a asibitin makon da ya gabata.

Dr Haruna Liman, Shugaban kwamitin bada shawara na asibitin, yace tuni sun damka jaririn ga mahaifiyarsa a Bauchi ranar Talata, rahoton kamfanin dillancin labarai NAN.

Yace:

"An sace jaririn ranar 21 ga Satumba, 2022 misalin karfe 4:30 na yamma yayinda mahaifiyar ke jinya a asibitin."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaba Buhari ya bayyana yadda sabbin shugabannin za su samu

"An ceto yaron yau 27 ga Satumba misalin karfe 1 na dare kuma yana cikin koshin lafiya."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun gode Allah da kokarin jami'an tsaron asibiti, jami'an hukumar DSS, yan sanda, yan sanda, da sauran hukumomin tsaro."

Jariri
An Ceto 'Yar Jaririn Da Wata Mata Ta Sace A Asibitin ATBU Bauchi
Asali: Facebook

Mr Liman yace tun an damke matar da ake zargi da sace jaririn.

Ya yi bayanin cewa hukumar asibitin zata karfafa makaman tsaronta.

Iyalan yaron da aka sace sun mika gosiyarsu ga shugabannin asibitin da jami'an tsaro.

Mata Tayi Shigar Ma'aikatan Lafiya, Ta Sace Daya Daga Cikin Tagwayen da Aka Haifa a Asibiti

Mun kawo muku cewa an shiga tashin hankali a dakin haihuwa na asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, inda aka sace daya daga cikin tagwaye da aka haifa.

A zantawarsa mahaifin tagwayen da aka haifa da Daily Trust, Ibrahim Dallami Khalid ya ce wata mata ta shiga dakin da matarsa take kwance ​​da tagwayen a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

An Yi Arangama Tsakanin Yan Sanda Da Yan Kalare A Gombe, Wasu Sun Jikkata

An shiga tashin hankali a dakin haihuwa na asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, inda aka sace daya daga cikin tagwaye da aka haifa.

A zantawarsa mahaifin tagwayen da aka haifa da Daily Trust, Ibrahim Dallami Khalid ya ce wata mata ta shiga dakin da matarsa take kwance ​​da tagwayen a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel