Dubun Wani Jami'in Soja Mai Saida wa Yan Ta'adda Makamai A Abuja Ta Cika

Dubun Wani Jami'in Soja Mai Saida wa Yan Ta'adda Makamai A Abuja Ta Cika

  • Yayinda yan Najeriya ke nuna shakku bisa ingancin jami'an tsaro, wani jami'in Soja ya shiga hannu
  • An damke Sojan dumu-dumu yana baiwa masu garkuwa da mutane hayar bindiga kirar AK-47
  • Ko a kwanakin baya ma dai an samu wasu sojoji (da aka kora) da kashe wani malamin addini

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya sun kama wani soja mai suna Nafiu, wanda yake aiki a barinkin sojoji na Muhammadu Buhari da ke Tungan Maje a babban birnin tarayya Abuja, bisa zarginsa da hayar tare da saidawa ƴan ta'adda makamai

Jaridar PUNCH Metro  ta ruwaito cewa an kama wanda ake zargin ne a makon da ya gabata a wani filin shakatawa da ke Ɗankogin Zuba, da taimakon ƙungiyoyin Banga dana sa-kai

Wata majiyar Jami'an tsaro ta shaida cewa, "sojan da aka kama yana ba masu garkuwa da mutane hayar bindigogi a kan kudi Naira 200,000 ko kuma N300,000.

Kara karanta wannan

Lokaci Ya Yi: Wata Budurwa Yar Shekara 18 Dake Kan Ganiyarta Ta Mutu a Hotel

Nafiu
Dubun Wani Jami'in Soja Mai Saida wa Yan Ta'adda Makamai A Abuja Ta Cika
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu Rahotanni sun ce "an kama shi ne bayan da wasu masu garkuwa da mutane da aka kama suka fallasashi"

"An bukaci su tuntube shi domin ya basu hayar bindigogin AK-47 akan kudi N3m kuma ya amince. Amma jami'an tsaron DSS sunyi nasarar damƙeshi ɗauke da bindiga ƙirar Ak-47 maƙare da harsashi lokacin da ake ƙokarin musayar ƙudin da makamai a zuba", Kamar yadda majiyar ta shaida.

Duk wani ƙokari kan jin ta bakin Kakakin hukumar tsaron farin kayan Mista Peter Afunanya bai yiwu ba, amma muna sake yunkuri dan jin ta bakin sa.

Kalli bidiyon damkeshi:

Asali: Legit.ng

Online view pixel