Buhari: Sai Na Magance Matsalar Tsaro Kafin Na Sauka Daga Mulki

Buhari: Sai Na Magance Matsalar Tsaro Kafin Na Sauka Daga Mulki

  • Shugaba Buhari a yau Juma’a ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen magance matsalar tsaro
  • Sannan ya tabbar da cewa burinsa shi ne barin Najeriya a matsayin ƙasa mai cike da zaman lafiya da wadata
  • A ƙarshe ya yaba wa shugabancin majalisun ƙasa ta fuskar irin kishin ƙasa da cigaban ƴan Najeriya da suke da shi

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alƙawarin cewa a cikin sauran kwanakin da suka rage masa a matsayin shugaban ƙasa, ƴan Najeriya za su ga sauyi game da matsalar tsaro.

Shugaban ya ba da wannan tabbaci ne a ranar Juma’ar nan da yake gabatar wa da Majalisar ƙasa tsararren jadawalin kasafin kuɗin Naira tiriliyan ashirin da dubu ɗari biyar da hamsin da ɗaya.

Kara karanta wannan

Kungiyar Fulani Ta Koka Kan Yadda Ake Cigaba da Yi Musu Kisan Gilla

Najeriya dai ta daɗe tana shan fama game da matsalolin tsaro da ya haɗa da na Boko Haram a Arewa maso Gabas da na tsaginta, wato ISWAP.

BUhari
Buhari: Sai Na Magance Matsalar Tsaro Kafin Na Sauka Daga Mulki Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

Sannan an samu yaɗuwar makamai wanda hakan ya sake samar da wata matsalar tsaron, inda aka samu ƴan bindiga masu kashe mutane da garkuwa da su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Irin wannan garkuwa kuwa ta shafi har ɗaliban makaranta a duk faɗin ƙasar nan, inda kuma sukan nemi kuɗin fansa daga hannun iyaye da hukumomi.

“Gwamnati a shirye take wajen cigaba da kare rayuka da dukiyoyi da kuma tabbatar da zuba hannun jari,” a cewar shugaba Buhari.

“Sannan za a ba wa ɓangaren tsaro muhimmanci a kasafin 2023 tare kuma da cigaba da ƙarfafa wa gwarazan jami’an tsaronmu; sojoji da ƴan sanda da duk wani jami’in tsaro,” a cewar shugaba Buhari.”

Kara karanta wannan

Lokaci Ya Yi: Wata Budurwa Yar Shekara 18 Dake Kan Ganiyarta Ta Mutu a Hotel

Haka kuma ya cigaba da cewa,

“Ina mai tabbatar muku da za mu shawo kan matsalar ƴan bindiga da garkuwa da mutane kafin ƙarshen lokacin mulkina.
Za mu daɗa ƙoƙari wajen mun bar tarihi na al’umma da ke cike da zaman lafiya da kuma arziƙi.”

Sannan shugaban ƙasar ya yaba wa shugabancin Majalisun ƙasa kan irin gudunmawar da suke bayarwa ga cigaban rayuwa ƴan Najeriya da tattalin arziƙinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel