Kece Ke Saukaka Min Lamurran Mulkina, Basarake Ya Zubawa Gimbiya Firdausi Bayero Kalamai

Kece Ke Saukaka Min Lamurran Mulkina, Basarake Ya Zubawa Gimbiya Firdausi Bayero Kalamai

  • Basaraken Oluwo na Iwo, Abdulrasheed Akanbi, ya rero kalaman soyayya ga matarsa Firdaus Bayero a ranar zagayowar haihuwarta
  • Basaraken yace ita ce ta mayar masa da mulkinsa tamkar cin tuwo saboda yadda ta saukake masa komai
  • Akanbi yace bashi da farin ciki a duniya da ya wuce ya bude idonsa da safe ya ga sarauniyar a gefensa

Abdulrosheed Akanbi, Oluwo na kasar Iwo, ya zuba kalaman yabo da soyayya ga matarsa Firdaus Bayero a yayin da ranar zagayowar haihuwarta.

A wallafar da yayi ta shafinsa na Instagram a ranar Juma'a basaraken yace Firdaus ce ke saukake masa lamurran mulkinsa har yake zama tamkar cin tuwo.

Sarki da Sarauniya
Kece Ke Saukaka Min Lamurran Mulkina, Basarake Ya Zubawa Gimbiya Firdausi Bayero Kalamai. Hoto daga Oluwo Of Iwo
Asali: Instagram

Oluwo ya kwatanta matasa da asalin sarauniya yayin da yayi mata addu'ar cigaba da shagalin karin shekaru a tare da junansu.

Kara karanta wannan

Ayiriri: Shirin Shagalin Auren Rukayya Dawayya da Afakallah Ya Kankama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwarki tawa kuma rabin raina. Allah yayi miki tsawon rai cikin koshin lafiya da wadata. Ina kaunar ki sosai har abada. Ina fatan mu cigaba da irin wannan murnar tare da juna, ke ce cikona a soyayya tun bayan da kika shigo rayuwata."

- Ya rubuta yayin da wallafa hotunan matarsa.

“Ke kika mayar da mulkina tamkar cin tuwo da izinin Oludumare da ya kawo asalin sarauniya cikin rayuwata.

“Ba ki da tamka, ni da ke tawaga ce, abokan juna ne masu karfin alaka. A kodayaushe kina baya na kuma ni ma zan kasance a tare da ke.

“Mafi kyawun ranata shi ne in tashi in gan ki a tare da ni kowacce safiya. Ina son ki san yadda nake ganin amfaninki da muhimmancin ki kan komai da kika yi saboda mu. Ina kaunar ku sosai kyakyawar sarauniyata Firdaus.”

Kara karanta wannan

Idan Nayi Nasara Zan Sake Fasalin Najeriya Tare Habaka Tattalin Arziki Kasar, Kwankwaso Ya Yi Alkawari

An daura: Sarkin Iwo ya angwance da Gimbiyar Kano, Firdausi bisa sadaki N1m

A wani labari na daban, Sarkin Iwo, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi (Telu 1), ya angwance da Firdaus Abdullahi, wacce jika ce ga marigayi mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero. An daura auren a gidan Madakin Kano, rahoton Daily Trust.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin akwai mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Babafemi Ojudu; Sarkin Yarbawan Kano, da Sarkin Yarbawan Zazzau, dss.

Wakilan Ango sun baiwa walliyin Amarya kudin sadaki milyan daya a gaban Madakin Kano, Yusuf Ibrahim Cigari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng