Yan Fashi Sun Kutsa Coci, Sun Lakada Wa Dattawa Duka, Sun Kwashe Kudade Da Wayoyin Salula A Wata Jihar Arewa

Yan Fashi Sun Kutsa Coci, Sun Lakada Wa Dattawa Duka, Sun Kwashe Kudade Da Wayoyin Salula A Wata Jihar Arewa

  • Wasu bata gari da ake kyautata zaton yan fashi da makami ne sun kutsa wani coci a Sariki-Noma, Jihar Kogi cikin dare
  • Maharan sun lakadawa dattawa da ke cocin duka, sun musu rauni da sanduna da kwalabe sannan suka sace kudi, wayoyi da wasu kaya
  • Wani ma'aikaci a cocin ya ce daga bisani yan bijilante sun yi nasarar kama biyu cikin bata garin yayin da ake cigaba da neman saura

Jihar Kogi - Yan daba da ake zargin yan fashi da makami ne sun kutsa cocin New Life Gospel Church da ke Sariki-Noma, a wajen garin Lokoja, babban birnin jihar, kuma sun sace kudade, wayoyi da kayan coci.

Faston cocin, Fasto Olorunfemi Ojo, ya shaida wa Daily Trust yan bindigan sun kai harin ne a safiyar ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Monama 15 Sun Mutu A Hatsarin Kwale-Kwale Yayin Girbe Masara A Gonakinsu Da Ambaliyar Ruwa Ta Cinye A Arewa

Harin Coci
Yan Fashi Sun Afka Coci, Sun Lakada Wa Dattawa Duka, Sun Kwashe Kudade Da Wayoyin Salula A Jihar Kogi. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Yadda harin ya faru

Ya ce yan daban, da adadinsu ya kai 15, sun kai harin ne a yayin da dattawa suke shirin yin addu'a na dare.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Ojo, awanni kafin harin, dattawan sun ga wasu maza uku suna kokarin tsallaka katangan cocin za su shiga wata makarantar frimare da ke katanga daya da cocin.

Ya kara da cewa jim kadan bayan ganin mutane ukun, yan daban da yawa sun kutsa cocin, sun fasa taga suka shiga ciki.

Bayan haka, yan daban suka afka wa dattawan suka musu duka da katako, kwalabe, da duwatsu suka raunata su.

Yan bijilante sun kama wasu daga cikin yan daban

Amma, faston ya ce yan bijilante sun kama wasu daga cikin maharan yayin da suka tafi kai hari a wani wurin cikin dare, ya ce jami'an tsaron suna cigaba da kokarin kamo maharan.

Kara karanta wannan

Ba Ta Bani Hakki Na: Miji Zai Saki Uwar 'Ya'yansa 8 Saboda Ta Daina Kwana Tare Dashi A Daki

Ya kara da cewa wasu ma'aikatan cocin sun tuntubi yan sanda kuma sun taho sun ga irin barnar da aka yi a cocin.

Martanin kakakin yan sandan Kogi

SP William Aya, mai magana da yawun yan sandan jihar Kogi ya ce kawo yanzu ba a masa bayani kan afkuwar lamarin ba.

'Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3

A wani rahoton, wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan fashin daji ne sun kai hari kan wani coci a jihar Kogi, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da masu ibada guda uku, Punch ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi a Cocin ECWA da ke Okedayo na garin Kabba, hedkwatar karamar Hukumar Kabba Bunu ta Jihar Kogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel