Monama 15 Sun Mutu A Hatsarin Kwale-Kwale Yayin Girbe Masara A Gonakinsu Da Ambaliyar Ruwa Ta Cinye A Arewa

Monama 15 Sun Mutu A Hatsarin Kwale-Kwale Yayin Girbe Masara A Gonakinsu Da Ambaliyar Ruwa Ta Cinye A Arewa

  • An gano gawar a kalla manoma guda 14 da suka nutse a ruwa yayin da suke kokarin girbe masara a Taraba
  • Wani mazaunin kauyen na Gwamtamu ya bayyana cewa kimanin manoma 50 ne suka shiga gonakin da ambaliyar ta cinye don girbe amfanin gonarsu amma gawar 15 aka gano
  • DSP Usman Abdullahi, mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Taraba ya ce kawo yanzu DSP na Gassol bai sanar da shi afkuwar lamarin ba

Jihar Taraba - Manoma guda goma sha hudu sun rasu a hatsarin kwale-kwale kuma ba a ga wasu da dama ba yayin da suke kokarin girbe amfanin gonansu a ambaliyar ruwa ta cinye.

Daily Trust Saturday ta tattaro cewa manoman su 12 ne ke cikin kwale-kwale suke zagayawa sune girbe masara da ruwa ya cinye lokacin da kwale-kwalen ya kife saboda ruwan sama da iska mai karfin gaske.

Kara karanta wannan

An gano wata maboyar 'yan bindiga a Arewa, an fatattaki tsageru, an ceto mutanen da aka sace

Kwale-kwale
Hatsarin Kwale-Kwale Ya Kashe Manoma 15 A Jihar Arewa, Ana Neman Wasu Da Dama Da Suke Nutse. Hoto: @daily_trust.

Lamarin, an gano ya faru ne a kauyen Gwamtamu a karamar hukumar Gassol da ke Jihar a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manoman, da aka ce sun fito daga kauyuka daban-daban kusa da jihar Benue, suna girbe masaransu ne da ruwa ta cinye baki daya.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana yadda lamarin ya faru

Nadabo Karal, wanda ya bayyana yadda abin ya faru, ya ce akwai kimanin manoma 50 a cikin kwale-kwalen.

Ya ce kawo yanzu gawar mutane 15 aka gano kacal yayin da ana cigaba da neman sauran.

Ya kara da cewa wannan shine hatsarin kwale-kwale mafi muni da ya faru a yankin da ya ritsa da manoma, ya ce biyu cikin gawarwakin yan gida daya ne.

Martanin yan sanda

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar yan sandan Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya ce ba su riga sun samu labarin daga DPO din Gassol ba.

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

Jinjiri Dan Wata 7 Da Mata 4 Sun Mutu A Hatsarin Kwale-Kwale A Jigawa

A wani rahoton, Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jigawa ta tabbatar da rasuwar jinjiri dan wata bakwai da mata hudu a hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Guri.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar, DSP Lawan Shiisu, ne ya tabbatar da afkuwar lamarin a Dutse, ranar Laraba, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel