Ba Ta Bani Hakki Na: Miji Zai Saki Uwar 'Ya'yansa 8 Saboda Ta Daina Kwana Tare Dashi A Daki

Ba Ta Bani Hakki Na: Miji Zai Saki Uwar 'Ya'yansa 8 Saboda Ta Daina Kwana Tare Dashi A Daki

  • Namitondo Mukwanu da matarsa sun shafe tsawon shekaru 12 tare kuma Allah ya albarkace su da haihuwar yara takwas, sai dai suna fuskantar matsaloli a gidan aurensu
  • Mijin ya lura da sabbin dabi'u daga matarsa bayan sun sauya muhalli inda suka bar garin da suke da zama
  • A cewar mutumin, kimanin shekara daya da rabi kenan da matarsa tayi kaura, inda ta koma kwana da yaransu a falo

Wani magidanci mai shekaru 46 a yankin Kabwe da ke kasar Zambia ya sha alwashin tsinke igiyar aurensu da matarsa ta sunnah saboda ta koma kwanan falo tsawon shekara daya da rabi.

Namitondo Mukwanu ya bayyana cewa tsawon watanni 18 kenan da matar tayi kaura zuwa falo cikin yaransu maimakon kwanan uwar daki.

Kara karanta wannan

Gemu bai hana ilimi: Bidiyon dan shekaru 38 da ya shiga firamare aji uku ya ba da mamaki

Mata da miji
Ya Saba Al’ada: Miji Zai Rabu Da Matarsa Ta Shekaru 12 Saboda Tana Kwana A Falo Tsawon Watanni 18 Hoto: ABN.
Asali: UGC

Jaridar ABN na Zambia ta rahoto cewa mijin ya bayyana lamarin a matsayin horo, wanda yasa shi yanke shawarar hanata tsara yadda zasu dunga kashe kudin wata.

Ya ce tun daga lokacin da suka sauya wajen zama sai ya lura da sabbin dabi'u a tattare da matar tasa, yana mai cewa sam bai cancanci horon da ake masa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Gidan nata ne, uwar dakin nata ne, me yasa take kwana a falo tare da yara?" Mukwanu yana mamaki.

Duk da ya zauna da matar, taki ta saurare shi, kuma ya ci gaba da shanye horon, wanda yace ya saba al'adarsu.

Magidancin ya sha alwashin sakin matar tasa tare da korata gidan iyayenta da zaran ya samu kudi.

Ma'auratan sun shafe tsawon shekaru 12 da aure kuma Allah ya albarkace su da haihuwar yara takwas tare.

Kara karanta wannan

Ni Kadai Iyayena suka Haifa: Matar da ke da Tattaba Kunne 101 ta Bayyana Hotunansu

Jama’a sun yi martani

Mukwae Shebz Mundia ta rubuta:

“Gaskiya abun bakin ciki ne tunda har ya kai ga haka. Sun haifi yara takwas a tsakanin shekaru goma sha biyu. Matar na kokarin ganin bata sake samun ciki bane. Rayuwa na wahala garesu duba ga cewar ba aiki matar ke yi ba. Za mu yi masu addu’a don kula da yaransu. Su dukka suna bukatar a wayar masu da kai.”

Prisca Matika ta yi martani:

“Matsaloli da dama da ba a magance ba a wannan aure, shin an nemi matar tayi bayani wannan halayya tata.”

Martha Nakanyika ta rubuta:

“Irin wannan namiji matsala ne, babu macen da za ta kai ga kauracewa shimfida idan komai na tafiya daidai, akwai lauje cikin nadi, su nemi magabatansu don suyi masu jagoranci.”

Ni Kadai Iyayena suka Haifa: Matar da ke da Tattaba Kunne 101 ta Bayyana Hotunansu

A wani labarin, Marguerite Peg Koller ta kasance ‘ya daya tilo a wajen iyayenta kuma tana matukar son samun kanne a lokacin da take tasowa.

Kara karanta wannan

Mai kamar maza: Bidiyon budurwa mai tuka tirela ya girgiza intanet, jama'a sun shiga mamaki

A cewar Marguerite, rayuwa a matsayin ‘ya daya akwai kadaici sosai kuma a kodayaushe tana addu’an Allah ya baiwa mahaifiyarta haihuwar wani dan.

A kullun ta kan fita waje wurin ‘ya’yan makwabta domin suyi wasa tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel