'Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3

'Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3

  • Wasu 'yan bindiga sun kai hari cikin wani coci a jihar Kogi inda suka hallaka wani mutum daya
  • Sun sace mutane uku cikin masu bauta a cikin cocin a yau Lahadi 19 ga watan Satumba, 2021
  • Rundunar 'yan sandan jihar sun tabbatar da faruwar lamarin, sun kuma ce suna bin diddigin 'yan bindigan

Kogi - Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan fashin daji ne sun kai hari kan wani coci a jihar Kogi, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da masu ibada guda uku, Punch ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi a Cocin ECWA da ke Okedayo na garin Kabba, hedkwatar karamar Hukumar Kabba Bunu ta Jihar Kogi.

Lamarin ya fau duk da cewa Gwamna Yahaya Bello ya bayyana jihar a matsayin mafi aminci a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar 'yan sanda sun kashe jami'ai, sun bakawa motarsu wuta

'Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3
Yahaya Bello, Gwamnan jihar Kogi | Hoto: premiumtimesng.com

Harin ya faru ne kwanaki bakwai kacal bayan da aka kai hari cibiyar kula da gyaran hali ta tarayya da ke Kabba; da kuma sace wasu manoman kaji guda uku a gonarsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ce masu garkuwar sun kai hari cocin ne yayin da ake gudanar da hidimar ranar Lahadi.

Cocin yana kusa da babban titin Kabba-Okene.

Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, DSP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa jami’an su na bin sawun wadanda ake zargin.

'Yan bindiga sun sace dalilan jami'a kwanaki kadan bayan sace malamansu

Wasu 'yan bindiga sun sace dalibai 10 na Jami'ar Jihar Abia, Uturu (ABSU) a hanyar Ihube zuwa ABSU, Daily Sun ta ruwaito.

Sace daliban na zuwa ne makonni bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da malaman jami’ar uku a kan hanyar Uturu/Isuikwuato.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyen Abuja, sun sace matan aure 2

Lamarin wanda rahotanni suka ce ya faru tsakanin karfe 5 na yamma zuwa 6 na yamma a ranar Asabar, ya jefa al’ummar jami’ar cikin rudani.

An ba da rahoton cewa motar bas ta jihar Abia da ke jigilar fasinjoji zuwa makarantar, SUV da mota kirar Hilux mallakar wani kamfani an same su babu kowa a ciki a wurin da lamarin ya faru, abin da ke nuni da cewa ba daliban kadai aka sace ba.

Wata majiyar tsaro ta ce kawo yanzu ba a san adadin mutanen da aka sace ba.

'Yan bindiga sun tare motar 'yan sanda sun kashe jami'ai, sun bakawa motarsu wuta

A wani labarin, akalla ‘yan sanda uku aka kashe a garin Onitsha, jihar Anambra sakamakon harin 'yan bindiga. Lamarin ya faru ne a hanyar Ukaegbu/Ezeiweka a Onitsha a safiyar Lahadi 19 ga watan Satumba, 2021.

An kuma kona wata motar sintiri kurmus ta jami'an da suka mutu. Wakilin Daily trust ya tattaro cewa wasu ‘yan sanda biyu sun jikkata a harin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace wani limamin Katolika, sun kashe mutane 11 a jihar Kaduna

Wani ganau ya tabbatar da faruwar lamarin amma jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda na jihar Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce har yanzu ba a sanar da shi ba batun ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel