Kotu Zata Raba Gardama Tsakanin Gwamnati Da ASUU Ranar Laraba

Kotu Zata Raba Gardama Tsakanin Gwamnati Da ASUU Ranar Laraba

  • Albishiri ga dalibai, da alamun zaman gida sakamakon yajin aiki zai zo karshe makon nan
  • Kotu ta sanar da cewa ranar Laraba mai zuwa za ta yanke hukunci kan karar gwamnati da ASUU
  • Tun watan Febrairu, 2022 kungiyar Malaman Jami'o'in Najeriya watau ASUU ta shiga yajin aiki

Kotun Ma'aikata Ta kasa ta sanar da ranar yanke hukunci kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar kan kungiyar Malaman Jami'a (ASUU).

Kotun ta zabi ranar Laraba, 21 ga watan Satumba, 2022, rahoton AIT.

Hakan ya bayyana ne a zaman kotun yau Litinin 19 ga Satumba, 2022.

A zaman, lauyan gwamnati ya jaddada bukatar gwamnati cewa kotu ta tilastawa lakcarori komawa bakin aiki.

Kotun
Kotu Zata Raba Gardama Tsakanin Gwamnati Da ASUU Ranar Laraba
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da PDP Ta Shigar Na Neman Haramtawa Tinubu Da Obi Yin Takara A 2023

Idan zaku tuna a zaman da akayi ranar Juma'a, lauyan Gwamnati, James Igwe, ya bukaci kotu ta gaggauta yanke hukunci kan wannan lamari saboda muhimmancinsa don dalibai su koma makaranta.

Igwe ya bayyana kotu cewa tunda yanzu ana shari'a, ya kamata Malamai su janye daga yajin aiki zuwa ranar yanke hukunci

Asali: Legit.ng

Online view pixel