Ni Fa Don Kudi Zan Yi Auren Nan: Budurwa Mai Shirin Aure Ta Bayyana

Ni Fa Don Kudi Zan Yi Auren Nan: Budurwa Mai Shirin Aure Ta Bayyana

  • Wata Yarinya mai shirin aure ta saki hotunan kafin bukinta amma tayi jawabi da ya baiwa mutane mamaki
  • Budurwar mai suna Habiba Gado ta ce ita don kudi za tayi aure kuma babu ruwanta da surutan mutane
  • Yan Najeriya sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan aure inda wasu sukayi san barka yayinda wasu sukayi suka

Wata budurwa mai shirin aure mai suna Habiba Gado ta janyo cece-kuce a kafafen ra'ayi da sada zumunta yayinda ta saki hotunan 'Pre-wedding' dinta da saurayin.

A hotunan da ta daura a shafinta na Facebook amma ta cire daga baya, Habiba tace ita da don kudi zatayi aure kuma wawan mutum ke aure don soyayya.

Habiba Gado
Ni Fa Don Kudi Zan Yi Auren Nan: Budurwa Mai Shirin Aure Ta Bayyana Hoto: Habiba Gado, Djbenzee Junior
Asali: Facebook

Tace:

"Ni don kudi zan yi aure, babu ruwana da surutan banza."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Kyakkyawan Karshe: Malamar Makaranta Ta Mutu Tana Tsaka Da Karatun Al-Qur'ani

Da farko ta goge jawabin a shafinta sakamakon caccakarta da wasu suka fara yi amma daga baya ta sake daurawa lokacin da Lindaikejiblog da Instablog9ja suka wallafa.

Saurayinta mai suna Djbenzee Junior shima ya daura bidiyon 'pre-wedding' shima na da ra'ayinsa na cewa 'wawa ke soyayya.'

Yace:

"Mutumin da ya samu mata ya samu arziki, kuma ya samu falala daga ubangiji."
"Ni dai na samu nawa."
"#NaMumuDeyLove2022."

Ra'ayoyin mabiyanmu

Gaddafi Bin Aminu yace:

Yadda Allah yasa ma Rayuwa Adadinta haka yasa ma dukiya Adadinta

Aleeyu Adamu Danhassan:

"Amma wannan tayi tunani me kyau, sallah ma dan lada ake yinta."

Zayyanu A Zarumi:

"Ana auren mutun dun kudinai amma bai kamata ace ita dakanta ta furta hakan ba Allah yasa mudace da masu summu so na gaskiya."

Adamu Kabiru:

"Wanda zai Aure ta ɗin yanzu kam shine mahaukaci ()()duk mace da tanuna kuɗi take so babu yadda za'ayi ta riƙe maka amanar Auren ka,ko wani daga makwabta idan yabata kuɗin zata baje masa hajanta."

Kara karanta wannan

Aminu Daurawa: Shawarwari 5 Da Na Ba Ummita Kafin Mutumin China ya kashe ta

Abdulhadi Sani Tofa:

"Faman kanat hijaratuhu.!!!! Lidduniya yasibuha."

Abba Lawan Fg:

"Gaskiya dayace indabata fadaba saidata aura acemata kuma mayaudariya ko"

Asali: Legit.ng

Online view pixel