Babu Wani Kulumboto da Sihiri da APC Zata yi Amfani da Shi Don Cin Zabe, Ortom

Babu Wani Kulumboto da Sihiri da APC Zata yi Amfani da Shi Don Cin Zabe, Ortom

  • Gwamna Ortom na jihar Binuwai ya bayyana cewa jam'iyyar APC babu shakka sai ta yi warwas a zaben 2023 da za a yi
  • A cewar gwamnan, babu irin sihirin da zata yi wa 'yan Najeriya ta ci zabe saboda ta gaza a mulkinta na shekaru bakwai da suka gabata
  • Ortom ya bayyana cewa, APC ta yi nasarar cika alkawarinta na kai Najeriya baya daga inda ta tarar da ita

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe, yace jam'iyyar APC ta matukar gazawa kuma babu abinda ta tabuka a shekaru bakwai da suka gabata na mulkinta.

Gwamnan yace akwai bukatar 'yan Najeriya su samo wata mafita daga kangin APC ballantana saboda irin mulkin da tayi a shekaru bakwai da suka gabata, TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan Ta'addan Boko Haram Kasurguman 'Yan Damfara ne, Shugaba Buhari

Jam'iyyar APC
Babu Wani Kulumboto da Sihiri da APC Zata yi Amfani da Shi Don Cin Zabe, Ortom. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda takardar da ya fitar ta hannun Nathaniel Ikyur, babban sakataren yada labaran Ortom ya bayyana, yace gwamnan yace APC zata yi warwas a zaben 2023.

"Sun cika alkawarinsu na kai Najeriya baya. Sun kai Najeriya fiye da kasa ma. Wannan babban abun kunya ne. Mu dake PDP burinmu bai wuce mu magance wannan barakar ba. Babu wani abu da zai yi mana hakan sai ikon Ubangiji, za mu kai ga nasara ta yadda zamu kawo cigaba."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Ortom yace.

"In har Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, zata iya aiki a matsayin kwararriya kuma bata bi bayan kowa ba kamar yadda tayi a zabukan Osun da Ekiti, ban ga yadda za a yi APC ta yi nasarar lashe zabe ba.
“Kasantuwa ta a siyasa tun daga farko, matakin jiha da na kasa sama da shekaru 40, babu wani sihiri da APC zata yi wurin ansarar zabe a 2023."

Kara karanta wannan

'Karyar Peter Obi Ta Wadatar Da Afirka Baki Daya', Fitaccen Jigon PDP Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP

- Yace.

Ortom yace APC tana rasa mambobi a fadin kasar nan inda yace da irin yawan jama'ar dake tururuwar komawa PDP daga APC, jam'iyyar za ta ga tasku nan babu dadewa.

Ana Tsaka da Rikicin Cikin Gida, Ayu Ya Mika Mulkin Jam'iyya Hannun Mataimakinsa, Ya Bayyana Dalilinsa

A wani labari na daban, duk da rikicin cikin gida na jam'iyyar PDP da ya ki ci balle cinyewa, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dr. Iyorchia Ayu, ya mika ragamar jam'iyyar hannun mataimakinsa na arewa, Umar Iliya Damagum.

Mai bai wa Ayu shawara na musamman a fannin yada labarai da sadarwa, Simon Imobo-Tswam, a yammacin Talata ya sanar da cewa Ayu zai bar kasar nan har zuwa karshen wannan watan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel