Katsina: 'Yan Sanda Sun Sheke 'Yan Ta'adda Masu tarin Yawa Bayan Artabu da Ruwan Wuta

Katsina: 'Yan Sanda Sun Sheke 'Yan Ta'adda Masu tarin Yawa Bayan Artabu da Ruwan Wuta

  • Jami'an 'yan sandan jihar Katsina sun ragargaji 'yan ta'adda kusan 30 a karamar hukumar Sabuwa ta jihar
  • Kamar yadda SP Gambo Isah ya sanar, 'yan ta'addan sun bayyana a babura inda suka tsare babban titin sabuwa zuwa Mararrabar Yakawada
  • An samo bindiga kirar AK-47 daya, ababen hawa hudu da sauran makamai inda wasu 'yan ta'addan suka tsere da raunika

Katsina - 'Yan ta'adda masu tarin yawa sun sheke lahira a karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina a ranar Laraba yayin da tawagar 'yan sanda suka far musu inda suka ci karo da kusan 30.

Vanguard ta rahoto cewa, an samo ikirar AK47 guda daya da kuma motocin 'yan ta'addan hudu da aka samo a wurin artabun kamar yadda kakakin rundunar 'yan sanda jihar, SP Gambo Isah ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Tukur Mamu Na Daukan Nauyin Yan Ta'adda, Inji Hukumar DSS

Katsina
Katsina: 'Yan Sanda Sun Sheke 'Yan Ta'adda Masu tarin Yawa Bayan Artabu da Ruwan Wuta. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

Kamar yadda rahoton 'yan sanda ya bayyana, sama da 'yan ta'adda 30 dake kan babura dauke da bindigu kirar AK-47 wurin karfe 2:45 na yammacin Laraba sun rufe hanyar Sabuwa zuwa Mararrabar Yakawada domin shirin yin fashi da garkuwa da jama'ar yankin kafin 'yan sanda sun bankado mugun shirin.

Bayan samun kiran gaggawa, DPO din karamar hukumar Sabuwa ta jihar yace sun gaggauta kam hanya inda ya jagoranci jami'an tsaro kuma suka far wa 'yan ta'addan tare da samun nasarar fatattakarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yawa daga cikin 'yan ta'addan an kashe su yayin da wasu suka tserewa da raunika.

Ana cigaba da binciken lamarin kamar yadda SP Gambo Isah ya bayyana.

Katsina: Yadda Rugugin Ruwan Kankara Ya Lalata Gonakin Jama'a

A wani labari na daban, wata gagarumar ruwan kankara ya lalata gonaki da gidajen jama'a a yankunan Dutsen-Kura/Kanya da Gozaki a karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Hotuna: Sojin Sun Ragargaji 'Yan Bindiga Har Maboyarsa, Sun Ceto Mutum 10

Malam Abdullahi Gozaki, wani mazaunin garin Gozaki ya sanar da Daily Trust cewa babu wani mutum daya da ya taba fuskantar irin wannan lamarin a yankin.

Yace gonakinsu, rufin gidaje da gilasan motoci duk suna lalace sakamakon ruwan kankarar da aka yi na tsawon mintuna.

Ya jero yankunan da lamarin ya shafa kamar haka: Gidan Danwada, Gidan Sabo, Kabalawa, Unguwar Tsamiya, Dandabo, Unguwar Maigarma, Uguwar Wanzamai da Unguwar Fulani.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel