Da Dumi-dumi: Diyar Sanata Ekweremadu Ta Roki Al’ummar Annabi Su Taimaka Mata Da Koda

Da Dumi-dumi: Diyar Sanata Ekweremadu Ta Roki Al’ummar Annabi Su Taimaka Mata Da Koda

  • Diyar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sonia Ekweremadu, ta roki jama'a da su taimaka mata da gudunmawar koda
  • Sonia bukaci duk wanda zai taimaka mata da aika sako dauke da suna, lambar waya, da adireshinsa zuwa adireshin helpsonialive@gmail.com
  • Matashiyar ta sha alwashin sadaukar da rayuwarta wajen kula da masu cutar koda idan har Allah ya tashi kafadarta

Sonia, diyar sanata Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, ta roki jama’a da su taimaka mata da gudunmawar koda.

Diyar dan majalisar ta yi wannan rokon ne a daidai lokacin da iyayenta suka shiga tsaka mai wuya a kokarinsu na ceto rayuwarta.

An kama Ekweremadu da matarsa a watan Yuni lokacin da suke kokarin samawa Sonia gudunmawar koda daga wani matashi.

Sonia da Ekweremadu
Da Dumi-dumi: Diyar Sanata Ekweremadu Ta Roki Al’ummar Annabi Su Taimaka Mata Da Koda Hoto: soniaekw
Asali: Instagram

An gurfanar da ma’auratan a gaban kotu kan zargin safarar mutum da kokarin cire wani sassa na jikin karamin yaro da bai balaga ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga bisani an bayar da belin Beatrice, matar dan majalisar yayin da shi kuma yake tsare har zuwa lokacin da za a sake zama kan shari’arsa a watan Oktoba.

A wata wallafa a shafin Instagram a ranar Litinin, Sonia, wacce ke zaune a UK, ta bukaci jama’a da su taimaka mata.

Wani bangare na wallafar na cewa:

“Ni Sonia Ekweremadu, ina rokon jama’a da su kawo mun dauki sannan su ceto rayuwata. Shekaruna 25 kuma na kammala karatun jarida a jami’ar Coventry. Na dakatar da karatun digirina na biyu a jami’ar Newcastle a 2019 lokacin da aka gano ina dauke da cutar koda.
“Iyayena na ta gwagwarmayar ceto rayuwata kuma sun kai ni asibitoci da dama, amma rashin lafiyan ya ci gaba kuma yana kara tabarbarewa. Ina raye a yau ne saboda ni’imar Ubangiji. Yanzu ina Landan, UK, ana yi mani wankin koda duk bayan awa 5 sau 3-4 a mako. Wannan duk daga aljihun iyayena ne saboda bana tsarin NHS.”

Ta kuma bukaci duk wanda ke da niyan bata gudunmawar koda da ya aika sako zuwa adireshin imel na helpsonialive@gmail.com sannan ya saka suna, lambar waya da adireshin imel da wurin zamansa.

Ta kuma ce duk wanda ke da niyan bata kodan ya sani cewa babu wani tukwici da za a basa kamar yadda yake a dokar Ingila da Wales.

A karshe ta ce za ta sadaukar da kanta zuwa ga taimakon mutanen da ke da matsalar cutar koda idan ta farfado.

Ga wallafar tata a kasa:

Sakamakon Binciken da Muka Gudanar Kan Tukur Mamu Yana Da Daure Kai, DSS

A wani labari na daban, hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ce sakamakon binciken da ta gudanar kan Tukur Mamu akwai ban mamaki sosai, Daily Trust ta rahoto.

Da take martani ga furucin da shahararren malamin Musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi yayi, hukumar ta ce ba za ta bari ta shagaltu ba.

Gumi ya zargi DSS da aikata ta’addanci, yana mai kalubalantar rundunar yan sandan ta farin kaya da ta saki Mamu, wanda ya kasance hadiminsa ko kuma ta gaggauta gurfanar da shi a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel