Bayan Kashe Mata N150,000 Ta Yaudareshi Ta Auri Wani: Wani Mutumin Yola Ya Bankawa Amarya Da Ango Wuta

Bayan Kashe Mata N150,000 Ta Yaudareshi Ta Auri Wani: Wani Mutumin Yola Ya Bankawa Amarya Da Ango Wuta

  • Magidanci ya sa bankawa Ango da Amarya wuta saboda amaryar ta yaudaresa bayan sun yi alkawarin aure
  • Amaryar ta mutu a asibiti sakamakon gobarar yayinda shi kuma Ango yana asibiti rai hannun Ubangiji
  • Hukumar yan sandan jihar na neman wanda aka baiwa kwangilan wannan aika-aika ruwa a jallo

Adamawa - Wani mutumin jihar Adamawa, Ibrahim Muhammadu, ya shiga komar yan sanda bayan kama shi da laifin bankawa Amarya da Ango wuta saboda matar ya yaudaresa.

Ibrahim Muhammadu, wanda dan asalin garin Gadawaliwol dake Jabbi Lamba, karamar hukumar Girei ta jihar ya baiwa wani kwangilan banka wuta ranar 6 ga watan Satumba, 2022.

Wannan abu ya faru makonni biyu kacal bayan auren Amaryar da Ango.

TheNation ta ruwaito cewa daga baya Amaryar ta mutu a asibiti sakamakon raunukan da ta samu a gobarar yayinda shi kuma Ango yana asibiti rai hannun Ubangiji.

Kara karanta wannan

Kwanaki 9 Da Bada Umurnin Damke Ado Gwanja, Safarau Da Yan TikTok 8, Har Yau Ba'a Kamasu Ba

Girei
Bayan Kashe Mata N150,000 Ta Yaudareshi Ta Auri Wani: Wani Mutumin Yola Ya Bankawa Amarya Da Ango Wuta Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa Ibrahim magidanci ne mai yara hudu amma ya fada rumbun soyayya da Amaryar har ya kashe mata kudi N150,000 bayan sun yi alkawarin aure

An tattaro cewa bayan amsan kudin hannunsa tayi tafiyarta ta auri wani.

Sai Ibrahim ya baiwa wani mai suna Ibrahim Savanna kudi N5,000 da kwanon shinkafa 4 don a kashe masa Amarya da Ango.

Bayan karban kudin da shinkafar, Ibrahim Savanna, ya bankawa gidan amarya wuta cikin dare.

Har yanzu ana neman Ibrahim Savannah Ruwa a Jallo

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Suleman Nguroje, ya tabbatar da aukuwan lamarin inda yace an kaddamar da bincike kuma za'a gurfanar da shi a kotu.

Ya bada tabbacin cewa lallai za'a hukunta mutumin kuma kada mutane su dau doka a hannu.

An Damke Isyaku da Usman Da Bindigogi 12 Da Harsasai 375 Zasu Kai Abuja

Kara karanta wannan

Kananan Yara 3 Sun Mutu A Ginin Da Ya Rufta A Jigawar Tsada

A wani labarin kuwa, jami'an hukumar hana fasa kwabrin kwayoyi NDLEA, a ranar Juma'a sun damke fasinjoji biyu da bindigogin PAP guda 12 da harsasai 374 a jihar Kogi, Arewa maso tsakiyar Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai NAN a ruwaito cewa fasinjojin biyu; Sagir Isiyaka (40) da Bello Shehu Usman na cikin motar J5 daga Onitsha kuma sun nufi shiga Abuja.

Kwamandan hukumar NDLEA na jihar Kogi, Abdulkadir Abdullahi-Fakai, yace jami'an sun damkesu ne yayinda suke sintiri a titin Okene-Lokoja-Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel