An Damke Isyaku da Usman Da Bindigogi 12 Da Harsasai 375 Zasu Kai Abuja

An Damke Isyaku da Usman Da Bindigogi 12 Da Harsasai 375 Zasu Kai Abuja

  • Jami'an tsaro sun kama wasu matafiya biyu dauke da bindigogi goma sha biyu da harsasai sama da 300
  • Jami'an NDLEA na binciken motocin ne don duba ko safarar kwaya akai sai suka ci karo da bindigogi
  • An mikasu ga hukumar yan sandan jihar Kogi domin gudanar da bincike kan su da makaman

Kogi - Jami'an hukumar hana fasa kwabrin kwayoyi NDLEA, a ranar Juma'a sun damke fasinjoji biyu da bindigogin PAP guda 12 da harsasai 374 a jihar Kogi, Arewa maso tsakiyar Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai NAN a ruwaito cewa fasinjojin biyu; Sagir Isiyaka (40) da Bello Shehu Usman na cikin motar J5 daga Onitsha kuma sun nufi shiga Abuja.

Kwamandan hukumar NDLEA na jihar Kogi, Abdulkadir Abdullahi-Fakai, yace jami'an sun damkesu ne yayinda suke sintiri a titin Okene-Lokoja-Abuja.

Kara karanta wannan

Jihar Kano Da Wasu Jihohin Arewa 5 Da Nike Da Tabbacin Zan Lashe: Tinubu

Ya kara da cewa tuni an kama mazajen biyu.

Anambra
An Damke Isyaku da Usman Da Bindigogi 12 Da Harsasai 375 Zasu Kai Abuja
Asali: Depositphotos

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabinsa yace:

"Wadanda aka damken biyu, Sagir Isiyaka (40) da Bello Shehu Usman (42) na tafiya cikin motar J5 Boxer daga Onitsha zuwa Abuja kafin damkesu."
"Yayinda aka binciki jakunansu, jami'anmu sun gano bindigogi da harsasai boye cikin buhu."
"Tun da lamarin bindigogi ne, da wuri muka garzaya da su wajen jami'an hukumar yan sanda don bincike."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel