Jerin Sunayen Tsaffin Gwamnonin Najeriya 31 Da EFCC Ta Kama Tun Kafuwarta A 2003

Jerin Sunayen Tsaffin Gwamnonin Najeriya 31 Da EFCC Ta Kama Tun Kafuwarta A 2003

 • A kalla tsaffin gwamnoni 31 ne hukumar yaki da rashawa na EFCC ta kama kan zargin almundahar kudi daban-daban
 • Gwamnoni ba za su kamu ba lokacin suna kan mulki saboda kariya da doka ta basu, don haka EFCC tana jira sai karshen wa'adinsu kafin ta kama su
 • Sashi na 308 na kundin tsarin mulkin kasa na 1999, da aka yi wa kwaskwarima, ya bada kariya ga shugabanni don kare darajar ofishin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'anatti, EFCC, tun kafuwarta a 2003 karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ta kama a kalla gwamnoni 30 a karshen wa'adinsu.

Bisa nazarin ayyukan hukumar, Legit.ng, ta tattaro muku adadin gwamnonin jihohi da hukumar ta kama tun kafuwarta.

Tsaffin gwamnoni
Jerin Sunayen Tsaffin Gwamnonin Najeriya 31 Da EFCC Ta Kama Tun Kafuwarta A 2003. Hoto: Hukumar EFCC.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hukumar yaki da rashawar tana binciken laifuka ne masu alaka da kudi, mafi yawancin almundaha ko karkatar da kudade.

Gwamnan da aka kama a baya-bayan nan

Gwamnan da aka kama na baya-bayan nan shine Willie Obiano, tsohon gwamnan Jihar Anambra.

An kama Obiano ne nan take bayan ya rasa kariyar da doka ta bashi saboda sunansa na cikin jerin wadanda ake zargi da rashawa.

Mafi yawancin gwamnonin an zarge su ne da bada kwantiragin jihohinsu ba bisa ka'ida ba da karkatar da kudin gwamnati zuwa aljihunsu.

Sashi na 308 na kudin tsarin mulki na 1999, da aka yi wa kwaskwarima, ya bada kariya ga gwamnonin jihohi don wasunsu na da kasafi da ya fi na wasu kasashen Afirka.

Ga jerin sunayen tsaffin gwamnoni 30 da hukumar ta taba kamawa:

 1. Willie Obiano na Jihar Anambra
 2. James Ibori na Jihar Delta
 3. Rochas Okorocha na Jihar Imo
 4. Bukola Saraki na Jihar Kwara
 5. Orji Uzor Kalu na Jihar Abia
 6. Peter Ayodele Fayose na Jihar Ekiti
 7. Gabriel Suswam na Jihar Benue
 8. Audu Abubakar na Jihar Kogi
 9. Abdullahi Adamu na Jihar Nasarawa
 10. Aliyu Akwe Doma na Jihar Nasarawa
 11. Joshua Dariye na Jihar Plateau
 12. Jonah Jang na Jihar Plateau
 13. James Bala Ngilari na Jihar Adamawa
 14. Murtala Nyako na Jihar Adamawa
 15. Ali Modu Sheriff na Jihar Borno
 16. Danjuma Goje na Jihar Gombe
 17. Jolly Nyame na Jihar Taraba
 18. Sule Lamido na Jihar Jigawa
 19. Aliyu Wammako na Jihar Sokoto
 20. Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara
 21. Theodore Orji na Jihar Abia
 22. Chimaroke Nnamani na Jihar Enugu
 23. Sullivan Chime na Jihar Enugu
 24. Ikedi Ohakim na Jihar Imo
 25. Godswill Akpabi na Jihar Akwa Ibom
 26. Diepreye Alamieyeseigha na Jihar Bayelsa
 27. Timipre Sylva na Jihar Bayelsa
 28. Lucky Igbinedion na Jihar Edo
 29. Olugbenga Daniel na Jihar Ogun
 30. Adebayo Alao-Akala na Jihar
 31. Rashidi Ladoja na Jihar Oyo

Asali: Legit.ng

Online view pixel