Bayan Kotu ta Wanke Jonah Jang Kan Zargin Damfarar N6.3b, EFCC Zata Dauka Mataki Mai Tsauri

Bayan Kotu ta Wanke Jonah Jang Kan Zargin Damfarar N6.3b, EFCC Zata Dauka Mataki Mai Tsauri

  • Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta sha alwashin daukaka kara kan shari'ar tsohon gwamna Jonah Jang
  • Kamar yadda mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ya bayyana, tuni hukumar ta fara kokarin daukaka kara kan hukuncin Mai shari'a C.L Dabup
  • A yau Juma'a ne alkalin babbar kotun jihar Filato ya wanke Jonah Jang da Yusuf Pam kan zargi 17 da suka hada da sace N6.3b na jihar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, tace zata daukaka kara kan hukuncin Mai shari'a C.L Dabup na babbar kotun jihar Plateau bayan ta sallama tare da wanke tsohon gwamnan jihar, Jonah Jang, da tsohon kashiyan ofishin sakataren gwamnatin jihar, Yusuf Pam.

Kakakin hukumar, Wilson Uwujaren, ya sanar da Daily Trust cewa hukumar ta fara bin ka'idojin daukaka kara da gaggawa a kan zargin damfara da take wa ma'aikatan gwamnatin biyu.

EFCC Eagle
Bayan Kotu ta Wanke Jonah Jang Kan Zargin Damfarar N6.3b, EFCC Zata Dauka Mataki Mai Tsauri. Hoto dag dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa, an sallama tare da wanke su biyun a babbar kotun jihar Plateau dake zama a Jos a ranar Juma'a kan zarginsu da laifuka 17 da suka hada da cin amana da waddaka da kudin gwamnatin jihar Plateau da ya kai N6.3 biliyan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga cikin abubuwan da ake zarginsu da shi akwai waskar da N2 biliyan wacce babban bankin Najeriya, CBN ta bayar domin taimakon matasa da mata kan kananan da matsakaitan sana'o'i da kuma waddaka tare da waskar da kudaden da aka ware domin hukumar SUBEB na jihar.

Kotun tayi watsi da dukkan zargin da ake wa tsohon gwamnan tare da tsohon kashiyan gwamnatin inda tace basu da makama.

Bincike Ya Fallasa Yadda Aka Saci Naira Biliyan 12 a Lokacin Tsohon Gwamnan PDP

A wani labari na daban, kimanin Naira biliyan 11.9 ake zargin sun bace daga asusun jihar Kwara tsakanin 2011 da 2019. Premium Times ta fitar da wannan rahoto.

Binciken kudin da aka gudanar, ya bankado yadda aka cire N2bn daga asusun gwamnatin Kwara ba tare da an yi wani aiki ko biyan kwangila ba.

Sakataren yada labarai na Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq watau Rafiu Ajakaiye, ya fitar da jawabi, yana zargin gwamnatin da suka gada da laifi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel