Har Abada Ba Zamu Yarda Da Takarar Musulmi da Musulmi Ba, Kungiyar CAN

Har Abada Ba Zamu Yarda Da Takarar Musulmi da Musulmi Ba, Kungiyar CAN

  • Shugaban CAN ya karyata labarin cewa ta karbi kudi hannun Tinubu don goyon bayan tikitin Musulmi-Musulmi
  • Kungiyar CAN tace sam bata sauya ra'ayinta game da takarar Asiwaju Tinubu da Kashim Shettima ba
  • Dan takarar shugaban kasa karkashin APC, Bola Tinubu, da Mataimakin, Kashim Shettima Musulmai ne

Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN tayi watsi da labarin cewa ta sauya ra'ayi game da takarar Musulmi da Musulmi bayan zamanta da dan takarar shugaban APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

CAN tace a daina siyasantar da halartar Tinubu bikin cikar Fada Matthew Kukah shekaru 70 da akayi a Abuja.

Shugaban CAN, Daniel Okoh, ya bayyana hakan a jawabin da mai magana da yawunsa, Luminous Jannamike, ya fitar, rahoton Punch.

Kungiyar CAN
Har Abada Ba Zamu Yarda Da Takarar Musulmi da Musulmi Ba, Kungiyar CAN

A cewarsa, sam kungiyar bata sauya ra'ayinta kan rashin amincewa da takarar Musulmi da Musulmi da jam'iyyar APC ke yi ba.

Kara karanta wannan

2023: Lokaci Ya Yi Da Arewa Zata Saka Wa Bola Tinubu, Shettima

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya karyata rahoton cewa kudin da aka bada wajen bikin Matthew Kukah asusun CAN za su shiga, riwayar Tribune.

A cewarsa:

"CAN ta samu labarin ana yada cewa Tinubu ya zauna da CAN kuma akace kungiyar kiristocin ta sauya ra'ayinta kan tikitin Musulmi da Musulmi."
"Wannan labarin kanzon kurege ne kuma ko wani mai hankali za'ayi watsi da shi. CAN ta jaddada cewa ba zata amince da tikitin Musulmi da Musulmi ba."
"Hakazalika CAN na Alla-wadai da kokarin sanya siyasa cikin halartan Tinubu taron ranar haihuwar Rabaran Mathhew Kukah a Abuja."
"Kudaden da aka bada asusun Cibiyar Kukah zasu shiga, basu da alaka da CAN. Saboda haka karya ne a ce an da shugabannin Kirista cin hanci don goyon bayan tikitin Musulmi."

Babu Ruwan Coci da Siyasar Jam’iyya, Shugaban CAN Ya Caccaki Wasu Fastoci

Kara karanta wannan

Kiristoci Zasu Samu Mukamai Masu Tsoka a Gwamnatin Tinubu, AIG Iyali

A wani labarin kuwa, Shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN), Dr Daniel Okoh, ya shawarci shugabannin kiristoci a fadin Najeriya da su kauracewa batutuwan da suka shafi siyasa.

Ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su yi karatun ta natsu wajen zaben shugabannin da za su mulke su a nan gaba, rahoton Punch.

Shugaban ya yi wannan kiran ne a garin Onitsha, ranar Lahadi 4 ga watan Satumba a bikin maulidin shekaru 75 na mu'assasin kungiyar Grace of God Mission International, Bishop Paul Nwachukwu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel