Kiristoci Zasu Samu Mukamai Masu Tsoka a Gwamnatin Tinubu

Kiristoci Zasu Samu Mukamai Masu Tsoka a Gwamnatin Tinubu

  • Shugaban Kungiyar yakin neman zaben Asiwaju Tinubu yace Kiristoci su kwantar da hankulansu
  • AIG Iyali ya ce gwamnatin Tinubu-Shettima zata baiwa mabiya addinin Kirista mukami masu tsoka
  • Tinubu zai kara da Atiku, Obi, da Kwankwaso a zaben shugaban kasan da zai gudana ranar 28 ga Febrairu

Abuja - Kungiyar Asiwaju Ahmed Bola-Shettima presidential support group ta bayyana cewa idan Bola Tinubu ya zama shugaban kasa, zai baiwa Kiristoci mukamai masu tsoka a majalisarsa.

Shugaban kungiyar, AIG Abdulsalami Iyaji (rtd), ya bayyana hakan a hira da manema labarai jiya a birnin tarayya Abuja, rahoton Vanguard.

A cewarsa, hakan zai kwantar da hankulan masu adawa da zaben Musulmi, Kashim Shettima, da Bola Tinubu yayi matsayin mataimakinsa.

Kara karanta wannan

2023: Jerin 'yan siyasar Najeriya da manyan kungiyoyin dake taimakawa kamfen din Tinubu

Shettima
Kiristoci Zasu Samu Mukamai Masu Tsoka a Gwamnatin Tinubu Hoto: APCNigeria
Asali: Facebook

Yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Akwai mukamai da yawa a gwamnati, Idan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Senator Kashim Shettima suka hau mulki, za'a baiwa Kiristoci mukamai a kowani sashe, kuma hakan zai kwantar da hankalin masu tsoron za'a Musuluntar da kasar."
"Abinda Tinubu da Shettima zasuyi zai kawar da tsoron tikitin Muslim-Muslim kuma mutane zasu daina la'akari da hakan wajen zabe, za'a daina sanya addini cikin siyasa."

AIG Iyali ya kara da cewa da dadewa babban matsalan Najeriya shine hauhawar farashi, rashin tsaro, yunwa, talauci, rashin abubuwan jin dadin rayuwa amma Tinubu zai magancesu kamar yadda yayi lokacin da yake gwamnan Legas.

Duk Bayaraben Da Yaki Zaben Tinubu Ba Dan Halas Bane, Jigogin APC

A wani labarin kuwa, mambobin kungiyar Next Level Consolidation Forum, wata kungiyar masoya Tinubu, sun bayyana cewa dan takaran kujeran shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, zai samu kashi 80% na kuri'un yankin Arewa maso yamma a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Babu Bayaraben Kirkin Da Zai Ki Zaben Asiwaju Bola Ahmed Tinubu A 2023, Shugaban Kungiyar Next Level

Shugaban kungiyar, Oladosu Oladipo, ya bayyana hakan ne a wani zama da suka yi a Ibadan, jihar Oyo.

Sun bayyana cewa yankin Yarbawa zasu yi duk mai yiwuwa don godewa Tinubu bisa ayyukan kwarai da yayi a matsayin gwamnan Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel