Zulum Ya Kayar Da Wike, An Alantashi Matsayin Gwarzon Gwamnan Shekara

Zulum Ya Kayar Da Wike, An Alantashi Matsayin Gwarzon Gwamnan Shekara

  • Gwamna Babagana Zulum ya sake zama gwarzon gwamnan shekara bisa iya jagorancin al'umma
  • Sama da yan Najeriya milyan daya suka zabi Zulum a kuri'ar da aka kada a yanar gizo
  • Gwamna Babagana Umara Zulum ya hau mulkin jihar Borno a shekarar 2019 bayan nasara a zabe

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagaba Umara Zulum, ya zama gwarzon gwamnan shekarar 2022 na lambar yabon iya shugabancin.

Zulum ya kayar da takwarorinsa irinsu gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, Nyesom Wike na jihar Rivers da kuma Seyi Makinde na jihar Oyo.

Ya ci zaben da aka gudanar tsawon kwanaki 14 a yanar gizo inda yan Najeriya suka kada kuri'a, rahoton Pulse.

Zulum ya samu kuri'u 1,028,469, yayinda mai biye masa Dave Umahi ya samu kuri'u 707,245, sai kuma Nyesom Wike da ya samu kuri'u 506,518.

Zulum
Zulum Ya Kayar Da Wike, An Alantashi Matsayin Gwarzon Gwamnan Shekara Hoto: Governor Of Borno
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gamayyar kasashen nahiyar Afrika AU da Cibiyar fina-finan Afrika sun yi na'am da wannan lambar yabo kuma za'a bada shi ranar 5 ga Nuwamba, a Abuja.

Ana bayar da lambar yabon ne ga shugabannin da jama'a suka amince da tsarin shugabancinsu da nasarorin da suka samu wajen taimakon al'umma.

Daga cikin wadanda zasu halarci taron baiwa Zulum lambar yabon sune tsaffin shugabannin kasa, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.

Kwankwaso: Zulum Ya Ci Taliyar Ƙarshe, NNPP Za Ta Ƙwace Borno A 2023

A wani labarin kuwa, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ayyana cewa jam'iyyarsa za ta kwace mulkin Jihar Borno daga hannun Gwamna Babagana Zulum, da ma wasu jihohi a kasar a 2023.

Kwakwaso ya yi wannan furucin ne a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, jim kadan bayan ya kaddamar da sakatariyar jam'iyyar a ranar Asabar.

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ayyana cewa jam'iyyarsa za ta kwace mulkin Jihar Borno daga hannun Gwamna Babagana Zulum, da ma wasu jihohi a kasar a 2023.

Kwakwaso ya yi wannan furucin ne a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, jim kadan bayan ya kaddamar da sakatariyar jam'iyyar a ranar Asabar

Asali: Legit.ng

Online view pixel