Shugaban Jam’iyya Ya Yarda Akwai Rikici a PDP, Ya Hango Abin da Zai Faru a 2023

Shugaban Jam’iyya Ya Yarda Akwai Rikici a PDP, Ya Hango Abin da Zai Faru a 2023

  • Shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu yana cikin tawagar da tayi wa Ibrahim Shekarau wankan tsarki a Kano
  • Dr. Iyorchia Ayu ya yi jawabi wajen karbar Ibrahim Shekarau daga NNPP, har ya yi kurin cewa PDP za ta karbe mulki
  • A cewar shugaban jam’iyyar adawar, PDP za ta lashe zabe a fadin Najeriya a 2023, duk da akwai masu jawo hatsaniya

Kano - A wani jawabi da ya yi wanda yake tamkar habaici ga Nyesom Wike, shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya gargadi ‘yan jam’iyyarsa.

This Day tace wannan jan-kunne ya zo ne a lokacin da jam’iyyar PDP ta karbi tsohon Gwamna, Ibrahim Shekarau wanda fice daga NNPP a jihar Kano.

Shugaban na PDP na kasa yake cewa mutanen Najeriya suka kafa PDP ba wasu daidaiku ba, a dalilin haka ne aka yi mata suna da jam’iyyar mutane.

Kara karanta wannan

'Albarka Ce' Tsohon Na Hannun Daman Buhari Ya Magantu Kan Sauya Shekar Shekarau Zuwa PDP

A jawabin da ya yi a makon nan, Ayu ya tabbatar da cewa akwai masu neman kawo matsala a PDP, ya kuma nuna bai da niyyar sauka daga kujerarsa.

PDP za ta ci zabe - Ayu

Punch ta rahoto shugaban babbar jam’iyyar hamayyar yace PDP za ta lashe zabe a kasar nan, har da Kudu maso kudu, yankin da Nyesom Wike ya fito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har ila yau, Ayu yace duk wani ‘dan jam’iyyar PDP yana da muhimmanci, sannan za suyi kokarin dawo da wadanda suka yi fushi, suka canza shekarsu.

Shugaban Jam’iyyar PDP
Shugaban PDP tare da Ibrahim Shekarau Hoto: @iyorchiayu
Asali: Twitter

“A matsayinmu na jam’iyyar mutane, ba mu jiran kowa. Za mu lashe zabe a ko ina, ba a Arewa kadai ba, za muyi nasara a Kudu da Kudu maso kudu.
Jam’iyyar PDP za ta lashe zabe a fadin kasar nan. A irin wannan lokaci a shekara mai zuwa, PDP ta kafa gwamnati. Babu wanda zai iya wargaza jam’iyya.”

Kara karanta wannan

Tinubu ne ‘Dan takara Mafi Cancanta, Amma Akwai Abin da Nake Tsoro - Shugaban APC

“Ba za a dauke mana hankali ba. Ka da ku damu da dukkanin masu neman jawo rigingimu.”
“Za mu shawo kan masu neman tada kafar baya. Za mu magance kalubalenmu. Kowane ‘dan jam’iyya yana da muhimmanci. Za mu jawo wadanda suka tafi.”

Sauran wadanda suka tofa albarkacinsu a wajen taron sun hada da Atiku Abubakar, wanda ya yi kira ga mutane su zabe shi, yace zai magance matsalolin kasar.

Ana rikici a APC?

Kun ji ana yada labari cewa shigowar Simon Lalong da Festus Keyamo cikin kwamitin yakin neman zaben APC ya fusata Shugaban Jam’iyyar APC.

Hakan ta sa wani babba a majalisar NWC na kasa, Nze Duru yace Bola Tinubu bai samu wata matsala da Abdullahi Adamu, kamar yadda jita-jita ke yawo ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel