Yadda Yan Bindiga Suka Datse Hannuwa Biyu Na Wani Mutumi a Jihar Zamfara

Yadda Yan Bindiga Suka Datse Hannuwa Biyu Na Wani Mutumi a Jihar Zamfara

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun sare hannuwan wani mutumi a jihar Zamfara
  • Ɗan uwan mutumin ya labarta yadda maharan suka shigo ta tsiya cikin gida suka aikata wannan ta'asa
  • A makon da ya gabata ne gwamnatin Zamfara ta yi ikirarin cewa ta fara shawo kan matsalar tsaro a faɗin jihar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Wasu Miyagun ƴan bindiga sun raba wani mutumi mai suna, Samaila Muhammad, da hannuwansa duka biyu a jihar Zamfara, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun farmaki mutumin da lamarin ya shafa ne bayan kutsa wa gidansa da ke ƙauyen Walo a yankin ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a jihar.

Ta'addancin Yan Bindiga.
Yadda Yan Bindiga Suka Datse Hannuwa Biyu Na Wani Mutumi a Jihar Zamfara Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ɗan uwan mutumin, Abdullahi Muhammed, wanda ya jikkata yayin harin, ya labarta yadda aka guntsule hannuwan ɗan uwansa duka guda biyun.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Ayarin Sojoji Kwantan Bauna, An Yi Kazamar Musayar Wuta, Da Yawa Sun Mutu

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yanzu haka ni da ɗan uwana Samaila muna kwance a Asibiti saboda na samu karaya a kafaɗa da ƙafa. Ƴan bindigan sun farmake mu wajen karfe 11:30 na dare, sun shigo da tsiya suka fara neman wurin da dabbobin mu suke."
"Mun fara jiyo surutu daga waje sai muka sunkuto Fitilu muka yo waje domin duba meke faruwa. Na ga ɗayan su na kokarin tattara kajin mu, sai na haske shi da fitila, ya harbe ni amma bai same ni ba."

Yadda suka sare wa mutumin hannu

Abdullahi ya kara da cewa ganin suna kokarin tattara dabbobin mu ne ya sa Sama'ila ya kalubalance su, su kuma suka masa wannan illa.

"Ganin suna kwashe mana Kaji ya sa ɗan uwana ya ƙalubalance su, ɗaya daga ciki ya zare adda ya datse masa hannu ɗaya, kafin ya yi wani motsin ceton kansa ya datse masa ɗayan hannun."

Kara karanta wannan

Wata Matashiya Da Ta Haihu Da Saurayinta Ta Sayar Da Jaririn Ɗan Mako Uku N600,000

"Yankin mu na fama da hare-hare masu muni kuma muna shan cin zarafi ciki har da wulakanta mana mata da kwanciya da su ta dole. Yanzu ana mana magani kuma muna samun sauki."

Wani mai alaƙa da iyalan gidan mutumin ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa wannan ba shi ne hari na farko da 'yan ta'addan suka kai musu ba

A cewarsa sun taɓa zuwa suka tattara musu shanu da awakai, "A karo na biyu ne ƙanin wanda aka guntule wa hannun ya ce su bi bayan su, mahaifiyar su ta hana su amma da tsautsayi ya kira su."

Mutumin, wanda ya nemi a ɓoye bayanansa saboda hali na tsaro, ya ce sun sare masa hannu ɗaya nan take, ɗayan kuma sai da aka je asibiti sannan aka ƙarisa cire shi.

"Yana da mata ɗaya da kuma 'ya'ya biyar, yanzu haka yana kwance a Asibitin Ƙauran Namoda ana kula da lafiyarsa."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Harbe Hadimin Jigon APC Har Lahira a Wurin Shagalin Karin Shekara

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Ayarin Sojoji Kwantan Bauna, An Yi Kazamar Musayar Wuta, Da Yawa Sun Mutu

Yan bindiga sun yi wa ayarin sojoji kwantan ɓauna, an yi kazamar musayar wuta a yankin ƙaramar hukumar Bungudu, jihar Zamfara.

Mazauna yankin da abun ya faru sun ce dakarun sun maida martani kuma sun kashe dandazon yan bindigan nan take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel