'Yan Bindiga Sun Kashe Hadimin Shugaban Karamar Hukuma a Legas

'Yan Bindiga Sun Kashe Hadimin Shugaban Karamar Hukuma a Legas

  • Wasu maharan sun farmaki wurin bikin karin shekara a Legas, sun bindige hadimin shugaban ƙaramar hukuma har Lahira
  • Kakakin yan sandan jihar Legas ya tabbatar da cewa harbin bindiga ne ya yi ajalin mutumin a a Asibiti
  • Shaidun da lamarin ya faru a kan idon su, sun bayyana yadda yan bindigan suka buɗe wa mahalarta bikin wuta

Lagos - Hukumar yan sanda jihar Legas ta ce wani hadimin shugaban ƙaramar hukumar Oshodi-Isolo, Kehinde Oloyede, ya mutu bayan samun raunin harbin bindiga.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan, Benjamin Hundeyin, ya shaida wa Premium Times cewa an harbi ɗan siyasan, Francis Oguntulu, a wurin bikin karin Shekara a Oshodi ranar Jummu'a.

Hukumar yan sandan Legas.
'Yan Bindiga Sun Kashe Hadimin Shugaban Karamar Hukuma a Legas Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hundeyin ya ƙara da cewa tuni aka kai lamarin sashin binciken manyan laifuka na hukumar yan sanda reshen jihar Legas.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yaudari manoma duk da kulla yarjejeniyar zaman lafiya, sun sace 16

A wata sanarwa da ta fito daga ofishin midiya na shugaban ƙaramar hukumar, Mista Olodeye ranar Lahadi, ta ce sai da aka sassari Mamacin daga bisani aka harbe shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma hukumar yan sanda ta ce abu ɗaya da zata iya tabbatar wa shi ne an harbi mutumin da bindiga, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Yadda harin ya auku

Mista Oloyede ya bayyana mutuwar ma'aikacinsa mai biyayya da wani babban lamari da ya sa shi kaɗuwa. Ya ƙara da cewa sauran mahalarta bikin karin shekaran sun ji raunuka.

"Mutanen da abun ya faru a idon su sun bayyana cewa maharan sun zo ba tare da ɓoye fuskukokinsu ba, suka buɗe wa mahalarta taron wuta, Oguntulu ya ji raunukan harbi da yawa hakan ya bar shi cikin mawuyacin hali."
"Mun yi babban rashin mutum mai biyayya kuma abokin aiki, labarin rasuwarsa ta jijjiga mu. Muna kira ga hukumar yan sanda ta binciko duk mai hannu a kisan ta hukunta shi domin ya zama darasi ga saura."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Uwan Ɗan takarar Gwamna a Jihar Shugaban Ƙasa

Sanarwa daga Ofishin Ciyaman ɗin ta kara da cewa tuni aka kai gawar Mamacin ɗakin aje gawarwaki na babban Asibitin Isolo.

A wani labarin kuma kun ji cewa Kasurgumin Ɗan Bindiga, Bello Turji, Ya Rungumi Zaman Lafiya a Zamfara

Mataimakin gwamnan Zamfara, Hassan Nasiha, ya ce ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, ya rungumi shirin zaman lafiya.

Kwamitin da gwamna Matawalle ya kafa ya zauna sulhu da kungiyoyin yan bindiga Tara a kananan hukumomi uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel