Gwamnatin Tarayya Na Shawarar Soke Kungiyar ASUU Gaba Daya

Gwamnatin Tarayya Na Shawarar Soke Kungiyar ASUU Gaba Daya

  • Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnati na shawarar haramta kungiyar ASUU gaba daya idan bata amince ta janye daga yajin aiki ba
  • Gwamnatin tarayya a zamanta ta karshe da Malaman jami'an tace ba zata biya albashin wata 5 wa ASUU
  • Malaman jami'ar kuwa sun ce muddin ba'a biyasu wadannan kudade ba, babu komawa aji

Abuja - Bayanai da aka samu a jiya sun nuna cewa Gwamnatin Tarayya na shawarar haramta kungiyar ASUU idan mambobinta suka ki janyewa daga yajin aiki duk da tagomashin da ttayi musu.

Tun watan Febrairu, Malaman jami'o'in Najeriya sun shiga yajin aiki bisa yarjejeniyar da gwamnati taki cikawa tun shekarar 2009 na karin albashi.

Daga cikin abubuwan da ASUU ke bukata akwai sakin kudin alawus, kudin gyaran jami'o'i, matsalar manhajar biyan albashi IPPIS.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kwadago ta Kasa ta Goyi Bayan ASUU, ta Bullo wa FG da Sabuwar Barazana

Ngige ASUU
Gwamnatin Tarayya Na Shawarar Soke Kungiyar ASUU Gaba Daya
Asali: UGC

ASUU ta hau dutsen 'Na Ki'

ASUU ta lashi takobin cewa sai gwamnati ta biyasu kudin albashin watanni biyar da sukayi suna yajin aiki kafin su koma Aji.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ita kuma gwamnatin tarayya tace ba zata biya wadannan kudade ba kamar yadda Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya bayyanawa manema labarai ranar Alhamis.

Vanguard ta ruwaito cewa majiyoyi da dama daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa idan ASUU taki janyewa daga yajin, gwamnati zata yanke shawarar soke su.

Daya daga cikin majiyoyin wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace:

"Saboda muhimmancin da Shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa Ilimi, ya amince da baiwa jami'o'i karin N100bn yayinda aka baiwa kwalejin Ilimi da na Fasaha watau Poly N57bn."
"Hakazalika gwamnati ta amince da karin albashi kashi 35% ga Farfesoshi kuma 23.5% ga sauran Lakcarori. Bugu da kari, gwamnati ta amince a biya N50bn kudin alawus ga ma'aikatan."

Kara karanta wannan

Salon Shigar Kashim Shettima Zuwa Taron NBA Ya Dauka Hankulan Jama'a

"Rashin kishin kasa zai zama idan ASUU taki janyewa daga yajin aikin saboda 'yayanmu su koma makaranta.
"Gwamnati na da zabuka da yawa idan ASUU taki amincewa. Daya daga ciki shine soke kungiyar ASUU wanda ke cikin kundin tsarin mulkin kwadago."
"Shugaban kasa na da ikon soke duk wata kungiyar da ta zama Ala-ka-kai ga kasa. A dokar, shugaban kasa na da ikon janye lasisin rijistar duk wata kungiyar da halayenta suka sha ban-ban da manufar kafasu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel