NBA Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Kan Lauyoyi Da Suka 'Sace' Wayoyin Salula Wurin Taron Ta A Legas

NBA Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Kan Lauyoyi Da Suka 'Sace' Wayoyin Salula Wurin Taron Ta A Legas

  • Kungiyar lauyoyi ta kasa, NBA, ta ce za ta hukunta wasu lauyoyi da suka sace wayoyin salula da barnata kaya a wurin taronta a Legas
  • A ranar Laraba wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta ya nuna wasu lauyoyi suna ta wawaso da sace kayayyaki a wurin taron a Legas
  • Rahotanni sun nuna cewa jinkiri da aka samu wurin rabon jakkuna da wasu kayayyaki wurin taron ne ya harzuka wasu lauyoyin suka hargitsa wuri

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Olumide Akpata, shugaban kungiyar lauyoyi, NBA, ya ce duk lauyan da aka samu da laifi wurin lalata rumfunan taro, sace wayoyin salula, da dukkan jami'ai, The Punch ta rahoto.

Akpata ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin babban taron kungiyar na kasa da ake gudanarwa.

Akpata Olumide
Kungiyar Lauyoyi Ta Ce Za Ta Hukunta Wasu Lauyoyi Sa Suka 'Sace Wayoyi' A Wurin Taronta A Legas. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Tausayi Da Jin Ƙan Talakawan Najeriya Ne Ya Hana Buhari Cire Tallafin Man Fetur, Keyamo

Ya kuma yi bayanin dalilin da yasa aka samu jinkiri wurin rabon jakkuna a yayin taron.

Ya ce:

"Babu wanda ya ce ba za mu fuskanci matsaloli a rayuwa ba amma abin da ke da muhimmanci shine yadda za mu warware matsalar cikin gaggawa.
"Yan uwa na lauyoyi, ina muku godiya sosai. Da fatan za mu samu cigaba."

A wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta a ranar Laraba, an ga lauyoyi suna lalata rumfuna a wurin taron da kwace kayayyaki a daren ranar Talata.

Lauyoyi da suka hallarci babban taron karo na 62 na NBA a ranar Talata sun yi koka kan karancin kayayyaki, inda wasunsu suka ce ba su samu jakkuna ba.

Wasu lauyoyin sun koka kan karancin kayayyaki duk da cewa sun tafi wurin tantancewar ba sau daya ba domin tambaya, hakan, a cewarsu ya fusata su.

Amma, an samu jinkiri wurin rabon kayan duk da yawan mutane da ke jira a kan layi.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnonin Najeriya sun ba lallai a yi zabe a wasu jiohohin Arewa ba a 2023

Daga bisani wasu lauyoyin sun gaza hakuri kuma suka far wa masu tsaro a wurin, suka fara wawason kaya da lalata abubuwa da sace kayayyakin taron.

A bidiyon, an ga wasu lauyoyi suna lalata rumfunan rajitsa da daukan abubuwan da suke so saboda karancin jakukunan taro.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel