Tausayi Da Jin Ƙan Talakawan Najeriya Ne Ya Hana Buhari Cire Tallafin Man Fetur, Keyamo

Tausayi Da Jin Ƙan Talakawan Najeriya Ne Ya Hana Buhari Cire Tallafin Man Fetur, Keyamo

  • Festus Keyamo, ministan kwadago da samar da ayyuka, ya bayyana dalilin da yasa Shugaba Muhammadu Buhari ya jinkirta cire tallafin man fetur
  • Keyamo ya ce saboda tausayi da jinkai da Buhari ke yi wa talakawan Najeriya shi yasa ya ce jinkirta cire tallafin har sai an dauki matakan rage musu radadi
  • Ministan ya ce a halin yanzu babu wani dalilin barin tallafin domin ba ta amfanar yan kasar sai dai yin gibe a tattalin arziki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Ministan kwadago da samar da ayyuka kuma shugaban kungiyar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Festus Keyamo, ya bada dalilin da yasa Shugaba Muhammadu Buhari ya jinkirta cire tallafin man fetur, rahoton This Day.

Ya ce saboda tausayin da shugaban kasar ke yi wa talakawan Najeriya ne. Keyamo ya ce Buhari na ganin ya kamata a saka wasu matakai da za su rage wa talakawa radadin cire tallafin.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Buhari ya yi Allah wadai da kisan gillan da aka yiwa Shehin Malami a Yobe

Festus Keyamo
Tausayi Da Jin Kan Talakawan Najeriya Ne Ya Hana Buhari Cire Tallafin Man Fetur, Keyamo. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma akwai yiwuwar yan Najeriya za su fuskanci wahalhalu a shekera mai zuwa, a yayin da Keyamo ya nuna alamar za a fara daukan matakan da za su kai ga cire tallafin a 2023.

Keyamo, a jawabin da ya yi wurin kaddamar da kungiyar 'The Progressives Forum' (TPF) a Abuja ya ce za a fara tattaunawa kan cire tallafin a 2023, a yayin da ya ce gwamnati yanzu ta dogara da harai daga FIRS da wasu don biyan albashi.

Kamar yadda Leadership ta rahoto, Ministan ya ce ba zai yi wu a cigaba da biyan tallafin man fetur ba, don yana yin gibi ga tattalin arzikin kasar.

Kalamansa:

"A matsayin mu na jam'iyya mai son cigaba, munyi imanin cewa dole a tallafawa talakawa da masu matsakaicin karfi. Shi yasa muke da tsarin conditional cash transfer. Wannan shine tsarin shugaba Muhammadu Buhari, tsarin APC.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Yace Zai Iya Tuka Mota daga Abuja Zuwa Kaduna Ba Jami'an Tsaron Lafiyarsa

"Idan da wani gwamnati ne a yanzu da muke magana, da babu tallafi. Amma Shugaba Buhari ya ce kafin mu cire, akwai bukatar mu dauki wasu matakan rage wa talakawa radadin. Saboda babu dalilin cigaba da biyan tallafin a yau."

Keyamo ya ce kasashen da suka cigaba kamar Amurka da Birtaniya sun kara kudin man fetur sau biyu zuwa hudu.

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel