Bidiyo: Yadda Aka Biya Dala 20,000 Kudin Kamun Diyar Sanata Sahabi

Bidiyo: Yadda Aka Biya Dala 20,000 Kudin Kamun Diyar Sanata Sahabi

  • An gudanar da shagalin kamun amarya Amina Ummi, diyar sanata Sahabi Ya'u da angonta Muhammad Auwal
  • A yayin shagalin, kawayen amarya sun nemi a biya dala 10,000 kafin su ba dangin angon damar ganin fuskar amaryarsu
  • Sai dai kuma, dangin Auwal sun ce dansu ya fi karfin haka inda suka biya zunzurutun kudi har dala 20,000 nan take

Zamfara - Kamar yadda yake bisa al’adar mallam Bahaushe a duk lokacin da ake bukukuwan aure, a kan yi kamun amarya inda dangin ango za su biya kawayen amarya wasu yan kudade kafin su barsu su ganta.

Hakan ce ta kasance a wajen shagalin kamun kyakkyawar diyar sanata Sahabi Ya’u mai wakiltan Zamfara ta arewa.

Kamun amarya
Bidiyo: Yadda Aka Biya Dala 20,000 Kudin Kamun Diyar Sanata Sahabi Hoto: surykmata
Asali: Instagram

Dangin ango Muhammad Auwal sun isa dakin taron inda kawayen amarya Amina Ummi suka nemi a biya dala 10,000 don amaryar tasu mai tsada ce.

Kara karanta wannan

Hotuna da Bidiyon shagalin Kamun diyar Sanata Sahabi Yau sun Dauka Hankali

Sai dai kuma dangin angon sun nuna cewa dansu mai tsada ne don aka suka biya kudin kamu dala 20,000 wanda ya yi daidai da naira 8,431,600.00 kudinmu na gida Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin bidiyon da shahararriyar MC mai yayi a yankin arewa Surayya Kofarmata ta wallafa a shafinta na Instagram mai suna surykmata an gano ta rike da farin takardar saka wasika cike da damin kudin da dangin angon suka biya.

Daga nan sai dakin taron gaba daya ya dauki sowa kafin yan uwan angon suka isa ga amaryarsu bayan kawayenta sun yi masu rakiya.

Kalli bidiyon a kasa:

Kwarya Tabi Kwarya: Bidiyoyi Daga Shagalin Bikin Aminu Tajuddeen Dantata Da Aisha Bello Dambazau

A wani labari makamancin wannan, tsohon ministan harkokin cikin gida, Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya, ya aurar da zukekiyar diyarsa, Aisha Dambazau.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin Shagalin Kamun Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

An daura auren Aisha da kyakkyawan angonta, Aminu Tajuddeen Dantata a ranar Asabar, 20 ga watan Agusta, a masallacin Al-Furqan da ke Alu Avenue, Nasarawa, jihar Kano.

Tajudden ya kasance jika a wajen shahararren dan kasuwan nan na Najeriya, Alhaji Aminu Dantata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel