Bidiyo: Wani Mutum Ya Fallasa Sabuwar Dabarar Da Ake Amfani Da Shi Wajen Damfarar Mutane Kudi
- Wani dan Najeriya ya gargadi mutane a kan sabuwar dabarar da yan damfara suka billo da shi na yiwa mutane fashin kudinsu a kan idonsu
- A yanzu masu damfara suna saka yagaggun kudi a tsakiyar kudade yayin ciniki ta yadda idan mutum ya kirga zai ga kudaden sun cika amma karya ne basu cika ba
- A cikin bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya an gano yadda bari daya na kudin suka yi kauri yayin da daya barin yake bai cika ba
Najeriya - Wani mutumi ya ja hankalin jama’a a kan wani sabon hanyan damfara da miyagun mutane suka bullo da shi don damfarar mutane kudinsu.
Mutumin ya yi bayanin cewa a yanzu yan damfara na biyan mutane kudade da basu cika ba yayin da suke yaudararsu ta yadda za a ga kudaden sun cika idan suka kirga su.
Ya yi misali da wasu damin kudi yan 1,000 don nusar da mutane halin da ake ciki.
A cikin bidiyon da shafin LIB ya wallafa, an gano mutumin yana kirga kudaden kuma sun kai N18,000 a karshe. Amma da ya juya kudin zuwa daya barin sannan ya kirga, sai aka ga N9,000 ne a karshe.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai kuma ya yiwa kudin filla-filla don nuna cewa akwai yagaggun kudi da aka jona ta tsakiya ta yadda kudin ya kara yawa idan mutum ya kirga daga bangare daya.
Ya shawarci mutane da su jujjuya kudadensu bayan sun gama kirgawa don tabbatar da ganin cewa lallai sun cika a duk lokacin da aka basu.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
icezick_cakes_and_pastries ta yi martani:
"Mafita shine kirgawa daya bayan daya ."
uc_beddingandcollections ta ce:
"Wannan ne dalilin da yasa a kodayaushe nake kirga duk kudin da aka bani kamar yadda kakata take kirga."
godson_92 ya ce:
"Baaba, yakamata ace mutumin da ke kawo duk wadannan tunanin ya rigada ya yi abu mai kyau da su."
solution_da_king ya ce:
"Najeriya....ta yaya kuke gano duk wadannan sabbin dabarun..."
glitzlingerie ta ce:
"Hatsarin da ke cikin sana'ar POS ya fi ribar da suke samu."
nnwaezee ta ce:
" Najeriya kasarku."
Bidiyo: Mai POS ya Fallasa Yadda Za a Iya Kwashewa Mutum Kudi Ba Tare da Saninsa ba
A wani labari na daban, wani matashi 'dan Najeriya ya samu jinjina da yabo daga jama'a bayan ya basu shawarar yadda zasu gujewa 'yan damfara.
Matashin ya bayyana cewa, yana sana'ar POS ne sama da shekaru biyar kuma za a iya amfani da wannan sana'ar wurin damfarar jama'a.
Asali: Legit.ng