Kamfanin Mai Na NNPC Ya Lissafa Ayyuka 10 da Ya Yi da N2.3trn Na Mai a 2022

Kamfanin Mai Na NNPC Ya Lissafa Ayyuka 10 da Ya Yi da N2.3trn Na Mai a 2022

  • Yayin da ake jiran alat, NNPC ya gaza tura ko anini ga asusun tarayya tun farin 2022, duk da irin tashin da mai ya yi kasuwannin duniya
  • Rashin tura wadannan kudade ga asusun gwamnati ya kawo matukar cikas ga tafiyar da ma'aikatun kudi na tarayya, jihohi da kananan hukumomi
  • Domin kare kai, kamfanin mai na NNPC ya ba da bahasin inda ya kai wadannan kudade daga farkon shekara zuwa yanzu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ya ba da bahasin dalilin da ya sa har yanzu bai tura ko kobo daga kudaden cinikin mai tun farkon 2022 zuwa yanzu ba.

A jadawalin da ya fitar, NNPC ya bayyana dalla-dalla inda kukaden suka yi a cikin wani daftarin FAAC na watan Yuli a kafar yanar gizo.

Daftarin ya nuna cewa, tsakanin man dan mai da gas, NNPC ya tara kudaden da suka kai akalla Naira tiriliyan 2.38 daga watan Janairu zuwa Yunin 2022.

Kara karanta wannan

Hikima: Fasihi ya kirkiri bandakin da mutane za su totsa toroso, sannan a biya su kudi

Kudin NNPC ya kare, an kashe kudi gaba daya na 2022
Kamfanin Mai Na NNPC Ya Lissafa Ayyuka 10 da Ya Yi da N2.3trn Na Mai a 2022 | Hoto: NNPC
Asali: Twitter

Mun kashe dukkan kudin, inji NNPC

Sai dai, wani hanzari ba gudu ba, domin NNPC ya ce babu sauran ko kobo daga kudin, saboda an kashe su a wasu ayyuka 10 a karkashin gwamnati.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ayyukan da NNPC yace ya yi da kudin sun hada da biyan tallafi, gyaran matatun mai, tsaro da tattala bututun mai, nemo shi kansa man, habaka harkar gas ta cikin gida da dawo da kudade.

Sauran ayyukan sun hada da bututun mai na Nigeria Morocco Pipeline, habaka samar da makamashin RED, kudaden fitar kayan mai da kuma kudaden da aka kashe wajen kula da bunkasa gas na NESS FEES.

Dalla-dalla yadda NNPC ya kashe kudade

Wani rahoton jaridar BusinessDay ya bayyana yadda NNPC ya ba da rahoton yadda ya kashe Naira tiriliyon 1.59 a tallafin mai.

Kamfanin ya yi nuni da cewa kudin tallafin mai ya tashi daga Naira biliyan 210 da aka kashe watan Janairun 2022 zuwa Naira biliyan 319 a watan Yunin 2022 yayin da farashin mai a duniya ya tashi.

Kara karanta wannan

Kudi Kare Magana: Bidiyon Katafaren Gida Da Wani Matashi Ya Kera Cikin Watanni 4

Kudin da aka kashe mafi yawa dai shine Naira biliyan 658.97 na recovery/cash call da aka bayyana da T1/T2.

Ba Lallai a Yi Zabe a Wasu Jihohin Arewa Maso Yamma Ba, Inji Gwamnonin Najeriya Ga Buhari

A wani labarin, wani sabon batu ya fito daga bakin gwamnonin Najeriya, inda suka bayyana ra'ayin cewa ba lallai a yi zabuka a wasu jihohin Arewa maso Yammacin kasar nan ba saboda kara dagulewar lamarin tsaro a shiyyar.

Arewa maso Yammancin Najeriya dai ta ta kunshi jihohi bakwai da suka hada da; Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, da Zamfara.

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, gwamnonin sun bayyanawa Buhari hakan ne a wani taron kan samar da wasu ka'idoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel