Da Duminsa: US zata Dawowa Najeriya $23m na Daga Kudin da Abacha ya Handama
- Gwamnatocin Najeriya da na Amurka sun kammala yarjejeniyar dawo da $23 miliyan na daga cikin kudin da Sani Abacha ya handama ya kai kasar
- An kammala yarejejniyar a ofishin ministan shari'a Abubakar Malami da jakadiyar Amurka Mary Beth inda kowanne yasa hannu a madadin kasarsa
- Kamar yadda Malami ya bayyana, idan an dawo da kudaden za a zuba su kan manyan ayyuka uku na gwamnatin tarayya a kasar nan
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Najeriya da gwamnatin Amurka sun kammala yarjejeniyar dawo da sama da $23 miliyan na kudin da Abacha ya handama ya boye a kasar.
Wannan yarejejniyar an sanya hannu kanta ne a ofishin ministan shari'a kuma antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, a ranar Talata
A yayin da Malami ya saka hannu a madadin gwamnatin Najeriya, jakadiyar Amurka a kasar Najeriya Mary Beth Leonard, ta saka hannu a madadin gwamnatin Amurkan, Channels TV suka ruwaito.
Kamar yadda Malami yace, idan an dawo da kudaden, za a zuba su a manyan ayyukan gwamnatin tarayya uku da ake yi da suka hada da babban titin Abuja zuwa Kaduna da gadar Niger ta biyu.
Asali: Legit.ng