Rashin Kudin Jirgi: Matashi Zai Tafka Asarar Daukar Nauyin Karatunsa Na N16m da Jami'a Tayi a Amurka

Rashin Kudin Jirgi: Matashi Zai Tafka Asarar Daukar Nauyin Karatunsa Na N16m da Jami'a Tayi a Amurka

  • Wani dalibi 'dan Najeriya mai suna Samrta Godwin Micah yana dab da rasa daukar nauyin karatunsa da aka yi mai darajar N16 miliyan
  • Wannan ya biyo bayan rashin kudin da Smart yake fama da shi na tikitin jirgin saman da zai kai shi Amurka inda zai fara karatu a jami'ar North Carolina dake Durham
  • Smart yana rokon 'yan Najeriya da su taimaka masa wurin tattara kudin jirgi domin ya tafi ya inganta rayuwarsa da karatun

Smart Godwin Micah, wani dalibin Najeriya wanda ya samu gurbin karatu domin yin digirinsa na biyu a Physics a jami'ar North Carolina dake Durham, USA.

Smart ya samu gurbin karatun kuma an dauka nauyin karatunsa kacokan mai darajar naira miliyan 16.

Smart Godwin
Rashin Kudin Jirgi: Matashi Zai Tafka Asarar Daukar Nauyin Karatunsa Na N16m da Jami'a Tayi a Amurka. Hoto daga @smartgodwin
Asali: Twitter

Babu kudin tikitin jirgi da na wurin zama

Sai dai, Smart ya gaza samun kudin tafiya da wanda zai fara karatunsa saboda a halin yanzu bashi da ko tikitin jirgin tafiya.

Kara karanta wannan

"A Taimaka min Don Allah, Ina Neman AIkin Yi," Makaho mai Kwalin NCE Ya Koka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayi kira ga 'yan Najeriya da su taimaka masa ya tafi Amurka kafin cikar wa'adin lokacin da ya dace ya fara karatun. Zai bukaci N2.470 miliyan domin tafiyarsa.

A Twitter ya rubuta:

"Na kashe kusan dukkan kudin da na mallaka wurin neman gurbin karatun kuma N300,000 ce ta rage min wanda ba zata isa in yi kudin jirgi ba da na wurin zama.
"Na yadda da taimakon ku, zan iya samun cikar burina na zama farfesan Physics kuma babban madubin dubawa ga wasu."

Legit.ng ta tuntubi Smart domin sanin dalilin da yasa daukar nauyin karatun bai hada da kudin tikiti da wurin kwana ba, yace shi makarantar ke tsammanin zai biya wadannan da kansa.

"A Taimaka min Don Allah, Ina Neman AIkin Yi," Makaho mai Kwalin NCE Ya Koka

A wani labari na daban, wani matashi 'dan Najeriya ya koka ga jama'a kan neman aikin da yake yi bayan ya kammala karatunsa na NCE.

Kara karanta wannan

Bincike Ya Tono Yadda Magu Ya Tafka Barna a EFCC, Ya ki Maido N48bn da Aka Sace

Matashin mai suna Hamza Aminu Abdullahi yana da kwalin NCE a bangaren karatu na musamman da na'ura mai kwakwalwa.

Hamza ba shi da idanu kuma ya kasa samun aikin yi tun bayan da ya kammala karatunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel