Bincike Ya Tona Yadda Magu Ya Tafka Barna a EFCC, Ya ki Maido N48bn da Aka Sace

Bincike Ya Tona Yadda Magu Ya Tafka Barna a EFCC, Ya ki Maido N48bn da Aka Sace

  • Kwamitin shugaban kasa da ya yi bincike a kan Ibrahim Magu, ya bankado yadda aka tafka barna
  • A lokacin yana ofis, tsohon shugaban na EFCC ya yi watsi da binciken zargin wasu sata da aka yi
  • Wasu sun saci kudi, amma Magu ya watsar da binciken, kuma ya saida kadarori ga mutanensa

Abuja - A lokacin Ibrahim Magu yana rike da hukumar EFCC, The Cable tace an gano ya yi watsi da wasu laifuffuka da ake zargin an saci N118bn da $309m.

Rahoton da aka gabatarwa shugaban kasa a Nuwamban 2020 shi ne, EFCC ta ki dawo da N48bn ga asusun gwamnati bayan EFCC tayi nasarar karbo kudin.

Jami’an EFCC sun yi nasarar karbe wadannan makudan kudi ne daga hannun barayin gwamnati. Wannan rahoto yana ofishin SGF, za a dauki mataki.

Kara karanta wannan

An kuma: Tururuwa ta cinye takardun kudaden da aka kashe a asusun inshora na NSITF

Jaridar tace daga cikin zargin da ake yi wa Magu shi ne ya taba kudin da aka karbe daga barayi, sannan ya saida wasu kadarorin da aka samu ga abokansa.

Ban san maganar ba - Lauya

Lauyan da yake kare tsohon shugaban na EFCC, ya ki cewa komai da The Cable ta tuntube shi. Wahab Shittu yace bai karanta wannan rahoto da ya fito ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A rahoton PCARA, an gano EFCC a karkashin jagorancin mukaddashin shugaban hukumar da aka dakatar, ta samu N46,038,882,509.87 na kudin kasar waje a matsayin kudin da aka karbe daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 22 ga watan Nuwamban 2018."
Magu.
Tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu Hoto:nairametrics.com
Asali: UGC

“EFCC ta fadawa PCARA cewa N504,154,184,744.04 ne asalin kudin da aka karbo a Naira, amma abin da aka ajiye a banki shi ne N543,511.792,863.47.”
“EFCC ba ta iya yi wa PCARA bayanin banbamcin N39,357,608,119.43 da aka samu a kudin ba.”

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya Fadakar da Mutane a kan Shugabannin da ba za a Zaba a 2023 ba

Ina gidajen da aka karbe?

Hukumar ta gagara tsaida magana daya a kan kadarori da gidaje da ta karbe. A wasu lokutan an ce akwai gidaje 836, daga baya aka ce 339 ko kuma 497.

Jaridar tace hukumar ta yi watsi da binciken zargi 14 da ake yi wa wasu manya. A haka aka yi watsi da binciken satar N117,972,209,035 da $309,151,419.

An gano a lokacin Magu yana kan kujerar shugaban EFCC, ya rika sabawa umarnin shugaban kasa, sannan an same shi da laifin sabawa umarnin kotu.

Otel da jirage sun yi kafa?

Akwai jiragen sama uku da EFCC ta karbe da ba a san inda suka shige ba. Haka aka yi da bayanan wasu manyan shaguna takwas da hukumar ta rufe.

Akwai otel 21 da EFCC ta rufe su a lokacin, yanzu takwas kadai ake da labarinsu. A gidajen mai 42 da kotu ta bada umarni a garkame, wasu sun yi dabo.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun yi Ram da Shugaban Dalibai Bayan Yace Minista Bai yi Wanka ba Ya Gana da Shugaban Kasa

Kwamitin ya gano wasu jiragen ruwa sun nutse dauke da kayan cikinsu, har yau babu labarinsu. EFCC ta raba wasu daga cikin jiragen ga sojojin ruwa.

An binciki Magu

A ranar Litinin, 6 ga watan Yulin 2020, aka ji labari kwamitin da shugaban kasa ya kafa ya binciki mukaddashin Ibrahim Magu, ya kama yin aiki.

Abubakar Malami SAN da hukumar DSS su na zargin Magu da karkatar da kudin da hukumar EFCC ta tattaro daga hannun barayi, ya yi facaka da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel