BudgIT ta Fallasa Jihohi 12 Dake Rike da Albashin Ma'aikata Na Tsawon Watanni

BudgIT ta Fallasa Jihohi 12 Dake Rike da Albashin Ma'aikata Na Tsawon Watanni

  • Hukumar BudgIT ta bayyana rashin jin dadin ta kan yadda jihohi 12 daga cikin 36 na kasar nan ke rike da albashin ma'aikata
  • BudgIT tace a sakamakon bincikenta na albashin 2022 na gwamnatin jihohin kasar nan, ta gano take hakkin ma'aikata da wasu jihohi ke yi
  • Daga cikin jihohin dake rike da albashin akwai Abia, Adamawa, Ebonyi, Ondo, Taraba, inda a kalla ma'aikata na bin bashi albashin wata 3

BudgIT, wata hukumar fasaha ta bayyana damuwarta kan yadda wasu gwamnatocin jihohi suka ki biyan albashin ma'aikata.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, BudgIT ta sanar da hakan a wata takardar da ta fitar ranar Alhamis wacce Iyanu Fatoba yasa hannu, mataimakin shugaban yada labaran kungiyar da sadarwa.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni: Ma'aikata a jiha ta na morewa, bana fashi ko jinkirin biyan albashi

Albashin Ma'aikata
BudgIT ta Fallasa Jihohi 12 Dake Rike da Albashin Ma'aikata Na Tsawon Watanni. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Hukumar tace sakamakon bincikenta na albasbin 2022 na kasa ya nuna cewa a kalla jihohi 12 ne ke rike da albashin ma'aikata har zuwa 28 ga watan Yulin 2022.

Ta yi kira ga jihohin da lamarin ya shafa da su gaggauta sauke hakkin wadanda suka dauka aiki ta hanyar biyansu albashinsu, Tribune Online ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"BudgIT ta bayyana rashin amincewarta bayan binciken da tayi a jihohi 36 na kasar nan ya bayyana cewa jihohi 12 ne rike da albashin a kalla wata daya na ma'aikata a ranar 28 ga watan Yulin 2022," takardar tace.
"BudgIT ta yi bincike kuma ta gano gwamnatocin jihohin da suka saba kin fitar da hakkin yarjejeniyar dake tsakaninsu da ma'aikata, lamarin da ke saka ma'aikata cikin tsananin damuwa da matsin rayuwa."

Yayin da binciken ya gano wasu jihohi da ke rike da albashi kamar jihohin Abia, Adamawa, Ebonyi, Ondo da Taraba. Akwai bashin shekaru uku ko kasa da hakan da ma'aikata ke bin su.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kungiyar COEASU Ta Jingine Yakin Aikin Ta Na Tsawon Kwana 60

"Misali, jihar Abia tana rike da albashin wata shida na makarantun gaba da sakandare na wata shida, Ebonyi bata biya 'yan fansho ba na wata shida. Ma'aikatan sakateriyar Taraba na korafin rashin daidaitaccen albashi na tsawon wata shida yayin da ma'aikatan makarantun gaba da sakandare da ungozoma a jihar Ondo ba a biya su ko sisi ba a watanni hudu da suka wuce."

Iniobong Usen, shugaban sashin bincike da shawari na BudgIT, yace biyan ma'aikata albashi yana daga cikin muhimman bangare na alakar ma'aikata da wadanda suka dauke su aiki, a matakin jihar ko tarayya.

Usen yace jinkiri a biyan albashi laifi ne da ke shafar aikin gwamnati inda ya kara da cewa rayuwar wasu ma'aikata da yawa ta ta'allaka ne kan albashi kuma hana su da gwamnatin ke yi ya nuna rashin daraja hakkin shari'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel