Babu Laifi Don Najeriya Ta Gwangwaje Nijar da Kyautar N1.4bn, Tsohon Shugaban NIS

Babu Laifi Don Najeriya Ta Gwangwaje Nijar da Kyautar N1.4bn, Tsohon Shugaban NIS

  • Tsohon Shugaban hukumar shige da fice, Mohammad Babandede, ya bayyana cewa babu aibu kan kyautar da Najeriya tayi wa Nijar
  • Babandede yace ba wannan karon bane Najeriya ta fara gwangwaje kasashen Afrika da irin wannan kyautar, duk kasashen ECOWAS suna hakan
  • Tsohon Shugaban NIS din yace kusancin Najeriya da Nijar yasa dakile rashin tsaron a kasar zai yi wa Najeriya matukar amfani

Tsohon Shugaban hukumar shige da fice ta kasa, Mohammed Babandede, yace babu wani aibu don Najeriya ta gwangwaje wata kasar nahiyar Afrika.

Wadannan karamcin kamar yadda yace suna da amfani saboda yana daga cikin tsarikan ECOWAS na cewa kasashen dake yankin su taimaki juna.

Ya bayyana wannan tsokacin ne a yayin tattaunawa da Premium Times a Twitter a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kungiyar COEASU Ta Jingine Yakin Aikin Ta Na Tsawon Kwana 60

Yana tsokaci ne kan rahoton kwanakin nan dake bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da siya tare da kyautar da ababen hawa na kimanin N1.4 biliyan ga kasar Nijar dake da makwabtaka da Najeriya.

Muhammad Babandede
Babu Laifi Don Najeriya Ta Gwangwaje Nijar da Kyautar N1.4bn, Tsohon Shugaban NIS. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A makon da ya gabata, ministar kudi, Zainab Ahmed, ta tabbatar wa da manema labarai cewa, gwamnatin Najeriya ta yi wannan kyautar ne ga jamhuriyar Nijar domin ta shawo kan matsalar tsaro kuma wannan irin kyautar da ake yi ga kasashe masu makwabtaka da Najeriya ba yau aka fara ba.

Ta kara da cewa, alhakin Shugaban kasan ne da ya dauka wannan matakin bayan ya natsu tare da duba lamarin.

Wannan labarin ya janyo maganganu daban-daban daga 'yan Najeriya wadanda suka dinga kira ga gwamnatin tarayya da daukar nauyin babban yaya ga kasashen Afrika ana tsaka da fama da matsalar kudin shiga, ga jami'o'in na yajin aiki na watanni.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya Shaidawa ‘Yanuwan Fasinjojin Jirgin da Aka Dauke Ya Bayyana

Babandede, wanda ya aminta da bayanin ministan, yace jamhuriyar Nijar tana daga cikin yankunan da 'yan Najeriya ke iya shiga kai tsaye, don haka duk wani tsari na inganta tsaro a kasar yana da amfani ga Najeriya.

Tsohon Shugaban hukumar shige da ficen yace "hayaniyar" dake tattare da wannan bayanin bashi da amfani saboda iyakar Najeriya ta fara ne daga inda ta Nijar ta kare tana cikin MNJTF.

A yayin da aka tambaye shi, me hakan zai kara ga Najeriya? Yace Najeriya zata amfana sosai amma dole ne kasar ta gyara tsarinta na kyauta da gudumawa.

"Mun taimakawa Namibia da wasu kasashe amma ba mu bi tsarikan saka hannun jari ba kuma hakan yasa 'yan Najeriya ke iya korafi."

A bangaren Seun Kolade, farfesan ya tuhumi gwamnatin tarayya kan yadda ta ki yin bayanin amfanin wannan gudumawar baya ga matsalar tsaro da tace.

Ya ce ya zama dole Shugaban kasa da gwamnatin su bayyana irin tallafin tsaron da yake son bayarwa da kuma dalilin da yasa za a siya motoci.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu : Shugaba Buhari ya Gana da 'yan uwan Wadanda Aka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel