Yajin Aikin ASUU: Yanzu Dankali Na Ke Sayarwa, In Ji Lakcaran Jami'ar Najeriya

Yajin Aikin ASUU: Yanzu Dankali Na Ke Sayarwa, In Ji Lakcaran Jami'ar Najeriya

Christiana Pam, wata lakcara a Jami'ar Uyo, Jihar Akwa Ibom, ta ce sana'ar sayar da dankali ta runguma domin kula da kanta tun bayan fara yajin aikin ASUU.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A ranar 14 ga watan Fabrairu ne ASUU ta fara yajin aikin gargadi na sati hudu. Kungiyar ta tsawaita yajin aikin da watanni biyu a ranar 14 ga watan Maris don bawa gwamnati daman biya musu bukatunsu. Ta sake tsawaitawa da sati 12 a ranar 9 ga watan Mayu.

Christiana Pam.
Yajin Aikin ASUU: Yanzu Dankali Na Ke Sayarwa, In Ji Lakcaran Jami'ar Najeriya. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

A makon da ta gabata ASUU ta sake tsawaita yajin aikin da wata daya, ta sha alwashin ba za ta janye ba sai an biya mata bukatunta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kungiyar ta ce dalilan da yasa ta ke yajin aikin sun hada da rashin biyan kudaden farfado da jami'o'i, allawus, da tsarin biyan albashi na UTAS a madadin IPPIS.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Amarya Ta Zage Ta Kwashi Garar Girki Kafin Ta Shiga Filin Rawa

A hirar da ta yi da Punch, Pam wanda hotunanta suka karade kafafen watsa labarai saboda sana'ar ta ta ce ta shiga halin rashin kudi a kwanakin farko na yajin aikin.

Yadda na tsinci kaina ina sayar da dankali

Christiana ta ce da farko ta saki jiki tana jira a janya yakin aikin cikin sati hudu amma da ta ga hakan bai faru ba kuma kudinta sun kare sai ta yanke shawarar ta koma gida Plateau har ma sai da ta ranci kudin mota.

"Iyaye na manoma ne dama, bayan sunyi murabus daga aiki sun koma gona. Da na koma gida na cigaba da zuwa gona tare da su da fatan bayan sati biyu za a janye yajin aiki. Tare muka yi sharar gona, shuka har da girbi. Daga nan na fara tunanin yadda zan samu kudi tunda ba zan iya tambayarsu ba saboda ni ya kamata ina tallafa musu. Daga nan na yi shawarar fara sayar da dankalin da muka noma a gonarmu kuma yan Akwa Ibom za su bukace su.

Kara karanta wannan

Na Rabu Da Mijina Saboda Ya Boya a Ban Daki Ya Barni A Hannun Yan Fashi Da Makami

"Sai da na sayar da wasu dankalin a Jos kafin in samu kudin tura sauran Jihar Akwa Ibom don in gwada hannu na. A nan ne aka ganni. Na yi imanin ka fara da abin da ka ke da shi. Abin da kake da shi ne za ka iya amfani da shi ka taimaki kanka. Na duba na ga ba abinda zan iya rike kaina da shi a wannan lokacin sai dankali."

Da aka tambaye ta yadda kasuwanci ke tafiya, Christiana ta ce tana samun riban N300 a kowanne buhu.

Yayin da ta ke fatan ganin an janye yajin aikin, ta yi kira ga sauran abokan aikinta su rungumi wani san'ar rike kansu.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel